Home Wasanni Wasan Tanis McHale Din Amurka Ta Doke Watson Din Ingila

McHale Din Amurka Ta Doke Watson Din Ingila

McHale Din Amurka Ta Doke Watson Din Ingila
5
0

Mchale‘Yar wasan tanis ‘yar Amurka, Christina McHale ta doke ‘yar kasar Ingila mai matsayi na biyu, Heather Watson a zagaye na farko na gasar tanis ta Abierto Mexicana Telcel da ake yi a birnin Acapulco na kasar Mexico.

Watson, mai shekara 23 tasha kashi da ci 4-6 da 6-0 da 7-6.

Da ma dai ‘yar wasan mai matsayi na 83 a duniya ta sha kaye a zagayen farko na gasar Australian Open, da aka yi a watan da ya gabata.

Mai matsayi na daya a wasan tennis ‘yar kasar Ingila, Johanna Konta ta samu damar zuwa wasan zagaye gaba, a inda za ta kara da ‘yar Croatia, Mirjana Lucic-Baroni.

 

Daga: BBCHausa

5

Daure ka/ki yi sharhi:
Hassan Abdulmalik Hassan Abdulmalik marubuci ne da ke da sha'awa ta musamman akan rubutun sharhin siyasa da tsokaci kan rayuwa da al'amuran da suka shafi al'umma. Ya na da kwarewa wajen rubutun zantukan fadakarwa da zaburarwa. Ya rubuta waƙe da harshen turanci babu adadi akan soyayya, aure, rayuwa, zamantakewa, addini, al'ada, shugabanci, zaburarwa, fadakarwa da sauransu.. A duk lokacin da Hassan ba ya rubutu, za ka same shi ya na karance-karance, kallon kwallon kafa/fina-finai, koyo ko kuma koyarwa
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Al\'ummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...