Home Labarai Duniya Firayi Ministan Birtaniya David Cameron Ya Yi Murabus

Firayi Ministan Birtaniya David Cameron Ya Yi Murabus

Firayi Ministan Birtaniya David Cameron Ya Yi Murabus
89
0

Sakamakon kuri’ar raba gardama da aka kada a kasar Birtaniya kan zama ko ficewa daga tarayyar turai ya nuna cewar kaso 52 na mutane Birtaniya ba sa son kasar ta Birtaniya da ta ci gaba da kasancewa a cikin kungiyar tarayyar turai, inda kaso 48 kuma suka kada kuri’arsu ga ci gaba da kasancewa a cikin kungiyar.

Ko shakka babu wannan matsayi da mutanen Birtaniya suka dauka ya saba da ra’ayin Firayi Ministan kasar David Cameron. Wannan dalili ya sa ya bayyana cewa zai sauka daga mulki a watan Oktoban Bana.

A cewarsa Mista Cameron, “bai dace na ci gaba da shugabancin Biritaniya ba tunda ‘yan kasar suna kan ra’ayi wanda ya yi hannun riga da manufofina.”

David Cameron ya yi fafutikar ganin kasar ta ci gaba da kasancewa a cikin kungiyar ta Tarayyar Turai, yana mai gargadin ‘yan kasar cewa duk wani abu sabanin hakan zai jefa tattalin arzikin kasar cikin mawuyacin hali.

Sai dai duk da haka ‘yan kasar ta Biritaniya kashi 52 sun zabi ficewa daga Tarayyar Turai, yayin da kashi 48 suka zabi ci gaba da kasancewa a cikin kungiyar.

89

Daure ka/ki yi sharhi:
Hassan Abdulmalik Hassan Abdulmalik marubuci ne da ke da sha'awa ta musamman akan rubutun sharhin siyasa da tsokaci kan rayuwa da al'amuran da suka shafi al'umma. Ya na da kwarewa wajen rubutun zantukan fadakarwa da zaburarwa. Ya rubuta waƙe da harshen turanci babu adadi akan soyayya, aure, rayuwa, zamantakewa, addini, al'ada, shugabanci, zaburarwa, fadakarwa da sauransu.. A duk lokacin da Hassan ba ya rubutu, za ka same shi ya na karance-karance, kallon kwallon kafa/fina-finai, koyo ko kuma koyarwa
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Al\'ummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...