Home Labarai Duniya Shi’a ta Sanya Shugabannin Al-Qaeda Da Na IS Cece Kuce

Shi’a ta Sanya Shugabannin Al-Qaeda Da Na IS Cece Kuce

Shi’a ta Sanya Shugabannin Al-Qaeda Da Na IS Cece Kuce
145
0

Shugaban kungiyar ta’addanci ta Al Qaeda mai da’awar jahadi a kasar Iraqi Ayman al-Zawahiri ya caccaki shugaban mayakan IS mai da’awar jahadi a kasar Syria Abu Bakr al-Baghdadi a wani sakon murya da ya fitar a jiya Alhamis.

Zawahiri na mayar da martani ne ga Baghadadi a sakamakon wata magana da ya yi na cewa kungiyar ta Al Qaeda ba ta goyon bayan hare-haren da ake kai wa ‘Yan Shi’a sannan kungiyar na kawance da shugabannin Kiristoci.

Su dai kungiyoyin na Al-Qaeda da na IS duk su na kiran kansu ‘yan sunni ne.

Bayan da ya kira Baghdadi makaryaci kuma mai yada frofagandar karya, Zawahiri ya kuma karyata zargin na Bahgdadi na cewa kungiyar ta Al-Qaeda ba ta kyamar shi’a.

Zawahiri ya ce ya yi kira ne da a dai na kashe fararen hula da sunan kai wa ‘Yan Shi’a hari, sannan ya karyata fadin cewa Kiristoci na iya zama abokan tafiya ga gwamnatin daular musulunci da suke fatar kafawa, inda ya ce abun da ya ke nufi shi ne Kiristoci na iya tafiyar da harakokinsu karkashin tsarin gwamnatin daular Islama.

Kungiyoyin Al-Qaeda da IS dai sun kashe mutane da dama a duniya da suka hada da mabiya shi’a da mabiya addinin kirista, kuma sun jagoranci daruruwan hare hare ta’addanci akan fararen hula.

Amurka da manyan kasashen duniya dai na neman shugabannin kungiyoyin ta’addancin biyu ruwa a jallo.

145

Daure ka/ki yi sharhi:
tags:
Jamila Mustapha Jamila Mustapha marubuciya ce ta harshen Turanci da Hausa kuma ma'abociyar karance karance a bangarorin ilimi da dama. A lokacin da ba ta rubuta, zaku same ta ta tsumduma baki da hanci cikin duniyar yanar gizo inda take kokarin gano hanyoyin da za'a iya amfani da kimiyarta wajen magance matsalolin al'umma.
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Al\'ummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...