Home Labarai Al’ajabi Tsohuwa Mai Shekaru 85 Ta Rataye Kanta a Kano

Tsohuwa Mai Shekaru 85 Ta Rataye Kanta a Kano

Tsohuwa Mai Shekaru 85 Ta Rataye Kanta a Kano
259
0

Wata tsohuwa mai kimanin shekaru 85 a duniya ‘yar kauyen Jar-Kuka da ke karamar hukumar Gezawa a jahar Kano ta rataye kanta a bishiya har lahira.

Rahotanni sun nuna cewa an yi ta neman tsohuwar mai suna Malama Salamatu Hassan har na tsawon kwanaki biyu ba a ganta ba, sai daga bisani aka tsinci gawarta a rataye a bishiya a sanyin safiyar jiya Lahadi

Salamatu dai na da ‘ya’ya 6 da jikoki da ba’a fadi adadin su ba.

Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano, DSP Magaji Musa Majiya, ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya ce binciken farko ya nuna masu tsohuwar na dan fama da tabin hankali.

tsohuwa

259

Daure ka/ki yi sharhi:
Jamila Mustapha Jamila Mustapha marubuciya ce ta harshen Turanci da Hausa kuma ma'abociyar karance karance a bangarorin ilimi da dama. A lokacin da ba ta rubuta, zaku same ta ta tsumduma baki da hanci cikin duniyar yanar gizo inda take kokarin gano hanyoyin da za'a iya amfani da kimiyarta wajen magance matsalolin al'umma.
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Al\'ummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...