Home Labarai An Gano Gawarwakin Sojoji Guda 16 A Cikin Wadanda Suka Bata

An Gano Gawarwakin Sojoji Guda 16 A Cikin Wadanda Suka Bata

An Gano Gawarwakin Sojoji Guda 16 A Cikin Wadanda Suka Bata
160
0

Rundunar Sojin Nijeriya ta sanar da cewa ta gano gawarwakin Sojoji guda 16 a cikin wadanda take nema, a bakin kogin Yobe.

Babban kwamandan rundunar ofireshon Lafiya Dole, manjo janar Lucky Irabor shi ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba.

Ya ce wadannan sojoji na cikin sojoji guda 46 da suka bace kimanin watanni 3 da suka gabata.

A cikin gawarwakin, har da ta Laftanal Kanal Yusuf,  kwamandan bataliya ta 223 mai kula da tankar yaki a cikin rundunar da ke yaki da Boko Haram.

Tuni aka binne gawarwakin a Makabartar Barikin Sojojin Maimalari.

A ranar 16 ga watan Oktobar shekarar da ta gabata ne aka sanar da bacewar sojojin a wata musayar wuta da suka yi da ‘Yan Boko Haram a yankin Gashigar Jahar Borno, inda da yawa suka afka cikin kogin na Yobe, domin su gujewa harsashai.

160

Daure ka/ki yi sharhi:
Jamila Mustapha Jamila Mustapha marubuciya ce ta harshen Turanci da Hausa kuma ma'abociyar karance karance a bangarorin ilimi da dama. A lokacin da ba ta rubuta, zaku same ta ta tsumduma baki da hanci cikin duniyar yanar gizo inda take kokarin gano hanyoyin da za'a iya amfani da kimiyarta wajen magance matsalolin al'umma.
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Al\'ummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...