Fifa Ta Yi Sabon Shugaba

0 49

InfantinoAn zabi dan kasar Switzerland Gianni Infantino a matsayin sabon shugaban hukumar kwallon kafar duniya, Fifa.

Infantino zai maye gurbin Sepp Blatter.

Ya samu kuri’a 115 a zagaye na biyu, inda mutumin da ke biye masa Sheikh Salman bin Ebrahim al-Khalifa ya samu kuri’a 27.

Yarima Ali bin al-Hussein ne ya zo na uku da kuri’a hudu, yayin da Jerome Champagne bai samu ko da kuri’a daya ba.

Tokyo Sexwale ya janye daga takarar kafin a fara kada kuri’a.

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...