Home Damben Gargajiya Dambe: Dan Kanawa Ya Buge Shagon Kaduna

Dambe: Dan Kanawa Ya Buge Shagon Kaduna

Dambe: Dan Kanawa Ya Buge Shagon Kaduna
913
0

Bahagon Dan Kanawa ya buge Shagon Musan Kaduna a turmin farko a wasan damben gargajiya da suka yi a ranar Lahadi a gidan damben Ali Zuma dake Dei-Dei a Abuja

Tun da farko Dan Kanawa da Nokiyar Dogon Sani ya so su taka wasa, amma Bahagon Abban Na Bacirawa ya ce da shi za a yi, haka ma shagon Shukuran ya ce yana sha’awar ayi da shi.

Sauran wasannin da aka yi a ranar Matawallen kwarkwada da Shagon Lawwalin Gusau ta shi suka yi canjaras a turmi biyu da suka taka.

Shi kuwa Fijo bai ba ta lokaci ba wajen buge Dakakin Dakaka a turmin farko, shima Shagon Salisu a turmin farko ya doke Shagon Dandigiri.

A wasan farko da Shagon Musan Kaduna ya yi, Autan Faya ne ya kai shi kasa a turmin farko, dambe tsakanin Shagon Bata da Niga babu kisa a turmi biyu da suka yi gumurzu.

An kuma yi gumurzu tsakanin Bahagon Alin Tarara da Shagon Sarka kuma turmi biyu suka yi babu wanda ya je kasa a tsakaninsu.

Daga karshe ne aka rufe filin da wasa tsakanin Matawallen Kwarkwada da Shagon Shukurana kuma turmi biyu suka yi Shagon Amadi ya raba wasan.

Daga:BBCHausa

(913)

Daure ka/ki yi sharhi:
Hassan Abdulmalik Hassan Abdulmalik marubuci ne da ke da sha'awa ta musamman akan rubutun sharhin siyasa da tsokaci kan rayuwa da al'amuran da suka shafi al'umma. Ya na da kwarewa wajen rubutun zantukan fadakarwa da zaburarwa. Ya rubuta waƙe da harshen turanci babu adadi akan soyayya, aure, rayuwa, zamantakewa, addini, al'ada, shugabanci, zaburarwa, fadakarwa da sauransu.. A duk lokacin da Hassan ba ya rubutu, za ka same shi ya na karance-karance, kallon kwallon kafa/fina-finai, koyo ko kuma koyarwa

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...