Wakilin Kudawa, Shagon Mada Ya Bayyana Cewa Zai Dawo Da Tagomashinsa

0 125

Shagon Mada dan wasan damben gargajiya mai wakiltar Kudawa ya ce zai dawo kan ganiyarsa a dambe.

Dan damben mai cikakken suna Kamalu Tanimu ya ce a yanzu a kwai shirye shiryen da yake yi don bunkasa wasan da yake yi.

Shagon Mada ya kuma ce damben gargajiya ya yi masa rana ya kuma samu alhairai da yawa, sakamakon hazakar da yake nunawa.

Ya kara da cewa shi dan kasuwa ne ya kuma iya dinki da sauran kasuwanci, idan ya yi ritaya daga wasan yana da sana’oin da zai yi

Shagon Mada ya kuma gode wa magoya bayansa da suke kara masa kwarin gwiwa a wasannin da yake yi, ya ce ba zai ba su kunya ba.

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...