Damben Gargajiya: Za A Bambace A Sokoto

0 74

Kungiyar wasan damben gargajiya ta kasa, ta shirya gagarumin wasa da za a yi a Sokoto a cikin wannan watan.

Shugaban kungiyar Ali Zuma ya ce sun zabi yin wasa a Sotoko ne, bayan da aka kammala wadda aka yi a birnin Minna a watan jiya.

Ana sa ran Ebola dan damben Kudu zai halarci wasan, domin bai wa Mai Takwasara fansar kisa.

A cikin watan Fabrairu ne a birnin Zaria Ebola, ya buge Mai Takwasara, a turmi na biyu a lokacin Ajon Anas Dan Sarkin Fawa.

Tuni kungiyar dambe ta jihar Kano karkashin jagorancin Dan Liti ta ce za ta ziyarci wasannin ne tare da ‘yan wasa Ebola da kuma Shamsu Kanin Emi.

Daga: BBCHausa

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...