Wasannin Zakarun Turai Za Su Koma Karshen Mako

0 31

BBC Hausa ta rawaito cewa, za a fara buga wasannin gasar cin kofin zakarun Turai a karshen mako daga shekarar 2021.

Hakan dai daya ne daga cikin shawarwarin da hukumar kwallon kafa ta Turai ta tattauna kan kara martaba gasar, da samun karin mabiya wasannin kungiyoyin nahiyar.

Sai nan da shekara biyar ne za a fara yin wasannin gasar a karshen mako, saboda yarjejeniyar da hukumar ta kulla ta nuna wasannin a talabijin a baya.

An fara buga wasannin gasar cin kofin zakarun Turai da a baya ake kira da European Cup a cikin tsakiyar mako tun a shekarar 1968.

Sai dai kuma idan aka dawo yin wasannin gasar a karshen mako za a yi la’akari da lokutan gasar wasannin kasashen hukumar da ake nunawa a talabijin.

 

Daga BBC

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...