Daga Zauren Fiqh: Halayen Masu Tsoron Allah

0 346

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.

Salati da aminci su tabbata bisa Maɓuɓɓugar hikimomi da ilimai na mutanen farko da Ƙarshe. Annabin da Allah ya aikoshi da gargaɗi da bushara da kuma tunatarwa ga masu tsoron Allah.. Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa da Sahabbansa masu tsoron Allah.

HALAYEN MASU TSORON ALLAH.

Muna bayani ne akan yanayin halayen da magabatanmu suka rayu akansa na tsananin tsoron Allah da kiyaye dokokinsa, da saurin tunawa da narkon azabarsa. Ba son komai ba, sai don mu karanta sannan mu yi koyi da su don mu gudu tare mu tsira tare.

Duk da cewar mafiya yawan rubuce rubucenmu da mu ke yi akan samu maciya amanar ilimi da suke kwafa suna editing suna goge wadansu abubuwan don cimma wani buri nasu. To amma wannan ba zai sa mu gaza wajen kokarin ilmantarwa da wa’azantarwa ba.

A cikin littafin Hilyatul Auliya’i na Abu Nu’aym Al-Asfahaaniy, ya kawo kissosi da hikayoyi da yawa irin wadannan. Kamar yadda shima Imam Ibnul Jawzee ya kawo wasu da yawa a cikin litattafansa kamar Sifatus Safwah, Uyoonul Hikayat da sauransu.

Wata rana ‘Aliyu ɗan gidan Fudhaylu bn ‘Iyadh ya yi sallah a bayan wani Limami sai Limamin ya karanta Suratur Rahman (Azza wa Jalla) bayan Fatiha, sai aka ji Aliyu din yana ta kuka a cikin sallar har aka idar.

Bayan an idar sai wasu suka tambayeshi “Mai yasa ka ke ta irin wannan kuka haka a sallah? Baka ji lokacin da Limamin ya karanto ayoyin rahama bane? A ciki har da bayanin ‘Yan matan gidan Aljannah? (HOORUM MAQSOORATUN FIL KHIYAAM)”.

Sai yace “Ai ayar azabar da ya karanto kafin wannan din, tunaninta ne ya shagaltar dani. (YURSALU ‘ALAIKUMA SHUWAAZUM MIN NAAR).

Ibnu Abi Zi’ibin yace wani wanda ya zauna tare da Umar ɗan Abdul-Azeez a lokacin yana gwamnan Madeena ya bamu labari cewa “Wata rana wani mutum ya zo gaban Umar ɗan Abdul-Azeez sannan ya karanta wannan ayar ta cikin Suratul Furqan (Wa Idha Ulquu minha…) :

“IDAN AKA JEFA SU A CIKIN WANI WAJE MAI KUNCI DAGA CIKINTA, ALHALI SUNA ƊAƊƊAURE, A WANNAN LOKACIN ZA SU RIKA KIRAN TAƁEWA AKANSU (WATO ƳAN WUTA KENAN)”.

Umar bn Abdil Azeez yana jin karatun wannan ayar sai ya fashe da kuka. Yana ta kuka, yana ta rusa kuka har sai da ya tashi ya shiga gida, kuma mutanen da ke tare dashi a wajen suka watse.

‘Ƴan uwa kunji fa masu tsoron Allah da gaske ba wai da gangan ba. Wadanda idan an karanta musu ayoyin Alqur’ani sai zuciyarsu ta kaɗu, idanuwansu su zubar da hawaye.

Abu Nouh Al-Ansariy ya ce : “Wata rana gobara ta tashi a gidan Imam Aliyu bn Al-Husain (Zainul Abideen) alhali shi a lokacin nan yana sallah, yana cikin Sujudah.

Mutane suna tsaye a gefensa suna ta kiransa “WUTA! WUTA!! GOBARA AKE YI!!! YA KAI JIKAN MANZON ALLAH (SAW)!!

Amma shi bai ɗaga kansa ba. Har sai da aka kashe wutar. Da ya idar sai aka tambayeshi “Menene ya ɗauke maka hankali haka? (Har akayi gobara a gidanka baka sani ba)”.

Sai yace “Waccan wutar ce ta lahirar”. (Wato tunanin wutar lahira ne yasa na kurumce na makance bana jin abinda ke faruwa kusa dani)”.

‘Ƴan uwa wannan fa Jikan Manzon Allah ne (saw). Babansa shine Al-Husain (rta) ɗaya daga Shugabannin Samarin gidan Aljannah. Hakanan Kakarsa ita ce Nana Faɗimah shugabar dukkan matayen halittu. Kakansa kuma shi ne Sayyiduna Aliyu Haidara, Khalifan Manzon Allah (saw) kuma ɗan uwansa (rta) amma duk da wannan ku dubi yadda yake jin tsoron Azabar Allah…!!

Ahmad bn Abil Hawariy yace “Na ji Abu Sulaiman Addaraniy (rah) yana cewa :

“Sau da yawa nakan ji kamar ga kaina nan a tsakanin wasu duwatsu guda biyu na wuta. Wani lokacin kuma sai in rika ji a cikin raina kamar gani nan ina nutso a cikin wutar Jahannama, Har sai na kai karkashinta. To duk wanda irin wadannan tunanin suka zama siffarsa, ta yaya zai ji dadin zaman duniya? (Ta yaya zai shagaltu da neman jin dadin zaman duniya?).

Imamu Ahmad bn Hanbal yace : “Abu Abdirrahman Al-Asadiy ya bamu labari cewa “Wata rana na tambayi Sa’eed bn Abdil Azeez (wani Tabi’iy ne) “Wannan wanne irin Kuka ne haka ya ke zuwa maka ko yaushe a cikin Sallarka?”.

Sai yace mun “Ya kai ɗan ɗan uwana! Menene dalilin yin wannan tambayar taka?”

Sai nace “Ya kai Baffana, Watakil Allah zai amfaneni da shi”.

Sai yace “Ban taba tashi don yin Sallata ba, face sai na ga kamar ga Jahannama nan a gabana”.

Sarrar Abu Abdillah yace “Na tuhumi ‘Ataa’u As-salamiy akan yawaitar kukansa a cikin Sallah. Sai yace mun “Ya kai Sarrar don me za ka tuhumeni akan abinda ba daga gareni yake ba?,

“Ni idan ina sallah ina tunowa da ‘Yan wuta da kuma Azabar Allah da Uƙubarsa yadda take sauka akansu. Sai zuciyata ta rika kwatanta mun yadda suke.

“To mai yasa zuciya ba za ta yi kuka ta yi ihu ba alhali tana ji kamar ga ta nan kamar an ɗaure hannayenta zuwa ga wuyanta, ana yi mata azaba?”

To ‘Yan uwa kun ji sallah irin ta masu tsoron Allah. Ba irin sallarmu ta zamanin nan ba. Mutum yana sallah a gefen titi amma yana ƙirga masu wucewa ta wajen. Ya san kalar tufafinsu, yana jin hirarrakinsu.

Ba irin sallar da za ka ga mutum yana sallah amma zuciyarsa tana kan wani abun daban ba. Ko kuma yana yi don riya da neman suna, Ko kuma sallar guggufiya (wato Ƙoton kurciya) Sallar da ko shi mai yinta ma yasan babu lada a cikinta ba.

An tuhumi Yazeedur Raƙƙashiy (rah) saboda yawaita kukan da ya ke yi a cikin sallarsa. Aka ce masa “Ai koda wutar lahirar nan saboda kai kaɗai aka yi ta, iyakar tsoro da firgitar da za ka yi kenan”.

Sai yace “Ai hakane ba’a halicci wuta ba, sai domin ni da abokaina, da kuma ‘Yan uwanmu daga Aljanu da Mutane”.

Yana gama faɗar wannan sai ya rika janyowa ayoyin cikin Suratur Rahman (Azza wa Jalla). Yayin da yazo kan ayar nan da Allah yake cewa:

“يطوفون بينها وبين حميم آن”

Sai ya miƙe yana yawo a tsakar gidansa yana kuka yana kuka har sai da ya faɗi sumamme!!

Rabi’atul ‘Adawiyyah (rah) wata baiwar Allah ce mai yawaita ibadah tare da gudun duniya. Wata rana da aka karanta wata aya a gabanta, a cikin ayar akwai ambaton wuta. Nan take Rabi’atul Adawiyyah ta faɗi ƙasa ta suma har zuwa wani lokaci mai tsawo sannan ta farfaɗo!.

Kun ji halin mutane na ƙwarai idan sun ji abinda Allah ya saukar na Alqur’ani sai ayoyin su yi tasiri a jikinsu da zuciyoyinsu. Da fatan Allah ya sa muyi koyi da su.

A nan za mu tsaya sai a darasi na gaba kuma zamu ɗora daga nan in sha Allah.

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...