Don Talakawa Mu Ke Aiki Kuma Za Mu Yi Musu Aiki Tsakani Da Allah-Honarabul Zakka

0 24
A tattaunawar da muka yi da kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jihar katsina Hon. Abdulkadir Ahmad Zakka, ya bayyana mana yadda suka tsinci kananan hukumomin Katsina cikin tsananin mawuyaci hali, da kuma irin yadda e-payment (tsarin biyan albashi a kimiyance) ta taimaka wajen gano ma’aikatan boge a kananan hukumomi.
Tare da wakilinmu Abdulkarim Papalaje.
Al’ummata: Mai girma kwamishina zamu so mu ji aikace aikacen hukumarka?
Zakka: Assalamu alaikum jama’a! Na gode wa Allah mahalicci da ya kaddara ni ne na zama kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jahar Katsina. Abu na farko da na ke so mutane su fuskanta ko su sani shi ne, ita sha’anin gwamnati ya kasu izuwa kaso uku, akwai gwamnatin tarayya, akwai gwamnatin jaha sai kuma gwamnatin kananan hukumomi wacce take a can kasa, tare da talakawa, wanda ya ke su ne gwamnati.
Kuma su wadannan talakawan su ne gwamnati, don su ne suka tabbatar da duk wata gwamnati da take kafafa, Allah ya sa ni ne nake shugabantar kananan hukumomi a nan jihar katsina. Game da tambayar da ka yi min na aikace aikacenta su ne kamar kula da albashin ma’aikatan kananan hukumomi da malaman makarantun firamare da masarautunmu na gargajiya da alawus dinsu na yau da kullum da wasu bangarori na gwamnati, kamarsu water board (ma’aikatar ruwa) da bangaren fansho, da service commission (sashen ma’aikata), wanda ake cewa local government service commission, wanda ya kunshi kula da da’ar ma’aikata, da shiryawa ma’aikata sanin makamar aiki, da kuma turasu ko canja su daga wata ma’aikatar zuwa wata, wato sauyin wuraren aikinsu, wanda duk hakkin ita wannan hukumar ne kula da duk abun da ya shafi ma’aikacin kananan hukumomi.
Sai kuma iyayenmu wato sarakunanmu, duk abun da ya shafi albashinsu, tun daga kan masu unguwanni, zuwa dagatai da hakimai da sarakunanmu, duk wannan   ma’aikatar ce ke da alhakin kula ko biyansu albashinsu.
AL’UMMATA: To mai girma kwamishina a wane hali aka tarar da ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu?
ZAKKA: Ahh.. alal hakika lokacin da muka shigo wanann ma’aikatar mun tarar da ita cikin wani irin hali na takaici, amma bara na gaya maka abun da muka gada. Da farko, mun tarar da naira miliyan goma sha daya a cikin asusun Hadaka na hukumar, wai miliyan goma sha daya a wannan hukumar. N,11,000,000. Sai kuma dan banzan bashi wanda bai da iyaka, anyi wasoso da kudin talakawa, amma saboda adalci da girmamawa da sanin dokokin irin na mai girma Rt Hon. Aminu Bello Masari, gwamnan katsina ya ce lalle ne mu tashi tsaye mu ga mun kare martabar al’ummar da suka zabemu, mu cika musu alkawuran da muka yi musu a baya. Sabanin wancan gwamnatin da ta shude, da ba su san abun da za su yi ba, don wani abu da ya faru, shi ne, su a lokacinsu ga uwar kudin, amma ba su san yadda za su sarrafasu su amfani talakawa ba, dan ba kishin talaka ma a ransu. Mu kuma yanzu ga tarin kishin da son yin aikin, amma ba kudin.
Amma yanzu da yardar Allah an fara samun saukin abubuwa. Don a yanzu haka da na ke yi maka wannan maganar duk a arewacin Nijeriya babu jahar da ba a bin ta bashi, in ban da jahar Katsina, don babu wata karamar hukuma da take binmu bashi. Mai girma Dallatun Katsina, Rt Hon Aminu Bello Masari, ya kira taron iyayen kasa na jahar katsina irinsu mai martaba Sarkin Katsina da Daura da tsoffin gwamnoni da ambasadodinmu da tsoffin ministoci da tsohon mataimakin gwamna kai da duk wani wanda aka san zai taimaka wajen ci gaban jahar katsina, don ba siyasa aka yi ba, babu ruwan mai girma gwamna da cewa wai dan jam’iyyar adawa ka ke duk da da akwai wadanda suka ki zuwa, saboda rashin kishin jahar katsinar a zukatansu, aka zauna aka tattauna, ya gaya musu irin halin da ya tarar da katsina a ciki, musamman ma kananan hukumomi, kazantar ta yi yawa, yana bukatar taimakonsu. Ka ga shi ne gwamna na farko a jihar Katsina da ya taba aikata wani abu irin wannan, aka yi maganganu masu amfani sosai a lokacin.
 
 
AL’UMMATA: To yanzu a wane hali kananan Hukumomin Jahar katsina ke ciki?
ZAKKA: To alhamdulillahi. Don ina mai tabbatar maka a watan farko da muka kama aiki, kasa biyan albashi muka yi, sai da muka je wajen gwamna ya cika mana naira miliyan dari biyu N200,000,000, aka tafi dari biyar, aka gangaro ana cika mana naira miliyan dari shida, kai akwai lokacinn da muke neman dari tara, ya koremu ya ce mu tafi, mu je mu nemi dari uku, shi dari shida kawai zai iya bamu daga cikin dari taran da muka nema.
Babu in da zamu je mu nema, don haka muka dawo muka zauna aka kukuta a hakan aka biya albashi, amma da muka kalli alawus-alawus na ma’aikata sai muka raba shi gida biyu, muka bibbiya rabi rabi, amma duk kudin da mai girma gwamna ya ke bamu rance ne ba kyauta ba. Wannan ya sa muka zage damtse, aka bazama neman kudaden shiga, muka shiga kasuwanninmu na kauyuka da tashohinmu da duk in da muka san suna karkashinmu. Tare da amincewar mai girma gwamna a kuma karkashin wancan zaman da aka yi da iyayen kasa, sun ce ya kamata a binciki yadda ake biyan tsarin albashin kananan hukumomi da L.E.A,wannan ne ya sa muka yi tsari aka shirya aka farad a kananan hukumomi guda tara, aka yi abun a bisa shiyya shiyya. A shiyyar katsina aka dauki nan Katsina, da Chiranchi da Batsari. A shiyyar Daura kuma aka dauki Mai Aduwa da Dutsi da Bindawa, a shiyyar Funtua kuwa an dauki Matazu da Sabuwa da Kurfi, muna fara wa sai muka ga ashe ga in da tsiyar take.
Wanann national policy din nan da ake yi yanzu na E-payment shi ya haddasa wanann matsalar da muke ciki yanzu, mutum baya aiki ba ya zuwa aiki, amma duk wata yana jin alert. Wasu ma babu su, wanda ake kira da GHOST WORKERS mu ka ce sam ba zai yiwu ba, sai mun yi duk yadda za mu yi mu ga mun dakile wanann barnar, sannan kuma yanzu haka muna nan muna bincike an kafa wani kwamiti na musamman da zai zakulo masu karban kudaden kananan hukumomi alhalin ba aiki suke ba. Duk kuwa wanda aka kama shi da cin kudin kananan hukumomi, wallahi sai mun buga sunansa a jarida sanann ya biya duka abun da ya ci ko kuma ya yi zaman gidan yari na iya adadin da alkali ya yanke masa, amma babu yadda za a yi muna ji muna gani ka ci kudin talakawa mu barka. Wallahi sai mun gurfanar da koma wanene a gaban shari’a.
 
 
AL’UMMATA: To mai girma kwamishina da me zaka rufe?
ZAKKA: Ina godiya ga Allah da ya bani wannan damar na rike da wannan hukumar, sai kuma mai girma Dallatun Katsina Rt Hon Aminu Bello Masari da irin fadi tashin da ya ke da mu kananan hukumomi, a duk sanda muka je masa da wani abu, zai tsaya ya sauraremu ya kuma tabbatar da an share mana kokenmu. Sai kuma jama’ar da suka zabemu. Ina mai sanar da ku cewa wannan gwamnatin ta sha bambam da gwamnatocin baya da aka saba yin su a jahar katsina, wanan gwamnatin taka ce, taki ce taku ce, tamu ce, gaba daya, kana da ruwa da tsaki, ka futo ka fadi ra’ayinka ka kawo gyara ko suka mai amfani. Don talakawa mu ke aiki, kuma za mu yi musu aiki, tsakaninmu da Allah. Na gode.

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...