Duniya Za ta Shiga Uku Idan Donald Trump Ya Zama Shugaba – Obama

8

Shugaban kasan Amurka Barack Obama ya yi kira ga mutanen kasar musamman ma ‘yan jam’iyyar Democrats da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin su zabi Hillary Clinton, inda ya yi masu gargadi cewa al’ummar duniya gaba daya za ta shiga uku idan dan takara jam’iyyar Republican Donald Trump ya zama shugaban kasar.

Ya fadi haka ne yayin da yake magana a wajen yakin neman zaben Hillary Clinton a jahar North Carolina da ke kasar.

Obama ya gargadi ‘yan jam’iyyar Republican da su guji jazawa duniya jangwamgwama. Ya kara da cewa Trump Hatsari ne ga ‘yancin ‘yan kasar na yin walwala.

Sai dai da alama wannan magana ba ta yi wa Donald Trump dadi ba, ya fadawa Obama da ya guji yi wa Clinton yakin neman zabe ya mayarda hankali kan mulkin kasar. Ya kuma kara da cewa su dai abun da suka sani shi ne babu wanda zai iya jure mulkin Obama na wasu shekara hudun.

Sannan ya shaidawa magoya bayansa cewa Clinton ta fara tabuwa a ‘yan kwanakin nan.

 

A ranar Talata mai zuwa ne dai mutanen kasar Amurka za su fito su kada kuri’unsu a zaben da ake ganin sai ya fi kowanne zafi a tarihin kasar, domin kuwa kuri’un ra’ayin jama’a game da ‘yan takarar a ‘yan kwanakin nan ya nuna sun yi canjaras.

 

You might also like More from author

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...