Home Cristiano Ronaldo Ya Lashen Kambin Ballon D’or

Cristiano Ronaldo Ya Lashen Kambin Ballon D’or

Cristiano Ronaldo Ya Lashen Kambin Ballon D’or
44
0

Dan wasan gaban Real Madrid Cristiano Ronaldo ya doke abokin takararsa Lionel Messi wajen lashe kyautar nan mai farin jini ta Ballon D’or karo na hudu.

A yanzu dan shekaru 31n na bayan dan wasan Barcelona Lionel Messi da kyauta daya ne kacal, bayan da Messi ya lashe a shekarar da ta gabata.

Dan wasan Atletico Madrid Antoine Griezmann shi yayi na uku a zaben.

A watan Janairun shekara mai zuwa hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA za ta bayar da nata kyautukan da suka hada da gwarzon dan kwallon duniya, gwarzuwar ‘yar kwallon duniya, kocin da ya fi yin fice, kociyar da ta fi yin fice da sauran kyautuka.

(44)

Daure ka/ki yi sharhi:
Hassan Abdulmalik Hassan Abdulmalik marubuci ne da ke da sha'awa ta musamman akan rubutun sharhin siyasa da tsokaci kan rayuwa da al'amuran da suka shafi al'umma. Ya na da kwarewa wajen rubutun zantukan fadakarwa da zaburarwa. Ya rubuta waƙe da harshen turanci babu adadi akan soyayya, aure, rayuwa, zamantakewa, addini, al'ada, shugabanci, zaburarwa, fadakarwa da sauransu.. A duk lokacin da Hassan ba ya rubutu, za ka same shi ya na karance-karance, kallon kwallon kafa/fina-finai, koyo ko kuma koyarwa
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...