Home PDP Ta Fidda Sharudan Wanda Zai Mata Takarar Shugaban Kasa A 2019

PDP Ta Fidda Sharudan Wanda Zai Mata Takarar Shugaban Kasa A 2019

PDP Ta Fidda Sharudan Wanda Zai Mata Takarar Shugaban Kasa A 2019
156
0

Babbar jam’iyyar adawa a Nijeriya, PDP ta fitar da wasu ka’idoji da sai wanda ya iya cikasu 100 bisa 100 ne zai yi wa jam’iyyar takarar shugaban kasa a shekarar 2019.

Sharuddan na jam’yyar PDPn sun hada da:

-Lalle wanda zai yi PDP takarar shugaban kasa a 2019 ya zamto mutum ne wanda ya dade yana hidimtawa jam’iyyar ba wai kawai wanda ya fara motsa jam’iyyar don yana son ya yi takara a 2019 ba

-Sai wanda akidu da kyawawan manufofin jam’iyyar ta PDP suka zama jini da jijiyarsa ta yadda zai iya bayyana manufofin jam’iyyar a aikace in har ya zama shugaban kasa

-Sai wanda ayyukansa na baya a wani matsayi ko mukami da ya rike suka nuna hazakarsa, aiki tukurunsa, sanin ya kamatansa da kokarinsa na yin aiki tare da abokan aikinsa

Sanata Walid Jibrin, Shugaban kwamitin dattijan PDP
Sanata Walid Jibrin, Shugaban kwamitin dattijan PDP
Shugaban kwamitin jam’iyyar PDP, Sanata Walid Jibrin ne ya bayyana hakan a ranar Asabar a Abuja

Sanata Walid ya ci gaba da cewa mun samu labarin cewa wasu da dama da suka bar jam’iyyar PDP na shirin dawowa jam’iyyar. Za mu karbe da zarar mun samar da warakar matsalolinmu. Za kuma mu bar kofar jam’iyyar a bude ga duk wanda ke son shuga jam’iyyar

(156)

Daure ka/ki yi sharhi:
Hassan Abdulmalik Hassan Abdulmalik marubuci ne da ke da sha'awa ta musamman akan rubutun sharhin siyasa da tsokaci kan rayuwa da al'amuran da suka shafi al'umma. Ya na da kwarewa wajen rubutun zantukan fadakarwa da zaburarwa. Ya rubuta waƙe da harshen turanci babu adadi akan soyayya, aure, rayuwa, zamantakewa, addini, al'ada, shugabanci, zaburarwa, fadakarwa da sauransu.. A duk lokacin da Hassan ba ya rubutu, za ka same shi ya na karance-karance, kallon kwallon kafa/fina-finai, koyo ko kuma koyarwa
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...