Home Duniya Wani Matashi Ya Yi Yunkurin Shiga Turai a Akwati

Wani Matashi Ya Yi Yunkurin Shiga Turai a Akwati

Wani Matashi Ya Yi Yunkurin Shiga Turai a Akwati
157
0

A jiya talata ne jami’an tsaron kan iyakar kasar Spain suka gano wani matashi dan kasar Gabon a cikin akwati irin wanda ake amfani da shi wajen zuba kaya musamman idan za’a yi tafiya.

Wata mata ce ta yi yunkurin tsallakewa da matashin mai shekaru 19 ta iyakar Spain da kasar Ceuta

Jami’an tsaron sun bayyana cewa matar da matashin duk sun fito ne daga kasar Morocco.

A kwanakin baya ma haka jami’an suka kama wasu ‘yan kasar Morocco guda biyu a yayin da suke kokarin tsallakar da wasu mutane zuwa kasar ta Spain a cikin akwati.

(157)

Daure ka/ki yi sharhi:
Jamila Mustapha Jamila Mustapha marubuciya ce ta harshen Turanci da Hausa kuma ma'abociyar karance karance a bangarorin ilimi da dama. A lokacin da ba ta rubuta, zaku same ta ta tsumduma baki da hanci cikin duniyar yanar gizo inda take kokarin gano hanyoyin da za'a iya amfani da kimiyarta wajen magance matsalolin al'umma.
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...