Majalisar Dattawa Ta Bukaci Shugaba Buhari Da Ya Janye Dokar Hana Shigo Da Motoci

3

Majalisar dattawan Nijeriya ta yi kira ga shugaba Buhari da ya janye dokar haramta shigo da motoci ta kan iyakokin kasar.

Majalisar dai ta ce dubban mutane ne za su rasa ayyukansu a sakamakon wannan doka.

Dokar hana shigo da motoci ta iyakoki ta fara aiki ne tun ranar 1 ga watan Janairun nan.

Sanatocin da suka gabatar da wannan bukata sun hada da Sanata Shehu Sani daga Jahar Kaduna da Kabiru Gaya daga Jahar Kano.

Sanatocin sun danganta wannan mataki da rashin adalci ga talakawa da ke samun na cin abinci ta wannan hanya.

Wasu sanatocin kuma na ganin abun da yafi kamata shi ne a sanya haraji akan shigo da motocin, ba a haramta kai tsaye ba kawai.

A don haka ne Majalisar ta bukaci shugaba Buhari da ya yi duba akan wannan koke.

You might also like More from author

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...