Wata Mata Ta Haifi ‘Ya’Ya 5 a Lokaci Daya Bayan Da Ta Shafe Shekaru 10 Ba Haihuwa

86

Wata mata a jahar Cross Rivers ta haifi ‘yaʼya 5 bayan da ta shafe shekaru 10 ta na fama da rashin haihuwa.

Matar ta haifi ‘ya’yan, mata 3 da maza biyu a asibitin Jamiʼar Calabar tsakanin karfe 10:50 da karfe 10:54 na safiyar ranar Litinin din da ta gabata.

Mahaifin yaran, mai suna Dr. Ekpo Edet, ya nuna matukar farin cikin sa, inda ya ce “Ina godiya ga Allah domin albarkar da ya yi mana. Wannan haihuwa na yara biyar a lokaci guda shi ne na farko a tarihin Jahar Cross River”.

Uwargidan Gwamnan Jahar Cross River, Dr Linda Ayade, ta kai wai iyayen ziyara, in da ta yi jawabi sannan ta yi masu tagomashi da kyautar naira miliyan daya.

Haka kuma ta yi wa ma’aikatan asibitin su ma kyautar Naira N500,000 a bisa rawar ganin da suka taka wajen haihuwar.

 

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...