HASSADA DA YADDA ZA A MAGANCETA A TSAKANIN AL’UMMA – Muhammad Albani Misau

113

GABATARWA

Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki, tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Sallam da Alayensa da Sahabbansa gaba daya da wadanda suka biyo bayan su da kyautatawa.

Wannan wani takaitaccen bayani ne akan abinda ya shafi HASSADA da yadda za a magance ta a tsakanin al’umma, nayi nazarin rubuta wannan takarda ne bisa matsaloli da suke shiga tsakanin al’umma a yanzu ta dalilin hassada, musamman daliban ilimi, da kuma masu hali, kai dama dukkan al’umma gaba daya, wannan yasa na ga ya kamata na yi rubutu don jawo hankalin ‘yan uwa na akan illar da Hassada take haifarwa da hanyar da za a magance ta a tsakanin al’umma gaba daya.

Allah na ke roka yasa wannan takarda ta zama hanya da sanadin magance wannan illar gaba daya ameen.

Fakiri mai neman gafara da kuma yardar Ubangijinsa.
MUHAMMAD MUHAMMAD
ALBANI MISAU.

(1). Ma’anar HASSADA:
Ita ce mutum ya yi burin gushewar wata ni’ima daga mai ita, ko dai ni’imar ta addini ko wani abun duniya.

(2). KARKASUWAR HASSADA:-
Mutane ta bangaren Hassada sun ka su zuwa gida biyu.

a. Akwai wanda ya ke burin ni’imar dan uwan shi ya gushe, kuma ya dobe shi da Ido (Kambun baka) sai ya cutar da shi saboda Hassada. Kambun baka gaskiya ne yana kai mutum zuwa ga kabari.

b. Akwai wanda yake hassada wa mutane, yana son ni’imar wanda ya ke wa hassadar ya kau (ya talauce) ko ni’imar ta dawo wajen sa, ko dukkan su su ta shi a tutar babu.

(3) HASSADA TAKAN SA MAI YINTA YA WUCE IYAKA DA ZALUNCI:-
Hassada takan sanya mai yinta ya wuce iyaka, har ta kai shi ga zalunci, da dukkan wasu abubuwa, har ta kai shi ga yin kisa.
Misali:-

a. Hassada ita ta sanya Qabila ya ka she ‘dan uwan sa Habila.
Allah Subhanahu wata Ala yana ba mu labari ya ce:-

“KUMA KA KARANTA MUSU LABARIN ‘YA’YAN ANNABI ADAMU DA GASKIYA. A LOKACIN DA DA SUKA BAYAR DA BAIKO, SAI AKA KARBA DAGA DAYAN SU BA A KARBA DAGA DAYAN SU BA”
Allah ya karba daga habila bai karba daga Qabila ba, sai Qabila ya ce, (Saboda Hassada wa ‘dan uwan sa):
“LALLAI NE ZAN KA SHE KA.”

Sai Habila ya ba shi amsa da cewa:

“ABIN SANI DAI, ALLAH YANA KARBA NE DAGA MASU TAQAWA. LALLAI IDAN KA SHIMFIDA HANNUNKA ZUWA GARE NI DOMIN KA KASHE NI, (ni) BAZAN ZAMA MAI SHIMFIDA HANNUNA ZUWA GARE KA BA, DOMIN IN KASHE KA, LALLAI NI, INA TSORN ALLA UBANGIJIN TALIKAI”. [Suratul Ma’idah aya ta 27-31).

b. Yusuf ‘yan uwan sa sun yi ikirarin su kashe shi, sai suka hadu akan suna ma su cewa:

“KU KA SHE YUSUFU, KO KU JEFA SHI A WATA KASA, FUSKAR UBAN KU TA WOFINTA SABODA KU, SAI KUMA KU KASANCE A BAYANSA MUTANE SALIHAI” [Suratu Yusuf aya ta 1-10].
Dalilin daya kawo haka shine Hassada, sai suka dauke shi suka jefa shi a Rijiya don ya mutu.
Wannan sakamakon Hassada kenan.

(4) HASSADA DABI’UN SHAIDANUN ALJANU DA MUTANE:-
Ka yi duba zuwa ga Iblis, Ya ga Annabi Adamu a cikin Aljannah kuma Allah ya halicce shi da hannunsa ya kuma busa masa rai, Mala’iku kuma suka masa sujjada. Sai Iblis (Shaidan) ya yi wa Annabi Adamu Hassada don ya fitar da shi daga Aljannah, Iblis ya bi hanyaoyin da zai bi har ya ci nasara, sai Annabi Adam ya fito daga aljannah, saboda wata hikima da Allah ya ke so.
Kaiton Iblis da ya kai wannan makurar har shela ya yi na ya ki da da Annabi adamu da zuriyar sa har ya zuwa ranar tashin Alkiyama.
Allah SWA ya ce:

“(Iblis yace) INA RANTSUWA DA HALAKARWAR DA KAYI MINI, ZAN KAWAR DA SU HANYARKA MADAIDAICI” [Suratul A’araf Aya ta 16].

(5). HASSADA TANA DAGA CIKIN ADON YAHUDAWA:-

Lallai yahudawa suna yin hassada wa mutane gaba daya, kuma suna yi wa muminai hassada a kebe.
Allah (SWA) ya ke ba mu labari “MAFIYA YAWA DAGA MA’ABOTA LITTAFI SUNA BURIN SU MAYAR DA KU, KAFIRCI DAGA BAYAN IMANIN KU, (miye dalili?) SABODA HASSADA DAGA RAYUKAN SU” [Suratul Baqara Aya ta 109].
ALLAH (SWA) ya sake cewa:-

“KO SUNA HASSADA WA MUTANE NE AKAN ABINDA ALLAH YA BA SU DAGA FALALARSA?” [Suratul Nisa’I Aya ta 54].

(6). HASSADA CUTA CE DAGA CIKIN CUTUTTUKA:-
Hassada wuta ce, tana cin zuciyar mai hassada kuma ta kan sanya mai aikata ta yin komai, mai hassada idan ya yi hassada wa mutum, sai ya yi ta bin diddiginsa yana bincike akan sa, alhali rahoto ko bincike akan wani haramun ne a musulunci.
“CUTUTTUKA NA AL’UMAR DA SU KA GABATA, ZAI FARU DA AL’UMA TA” Sai (Sahabbai) suka ce: Ya Manzon Allah menene cututtukan al’umar da suka gabata?. Ya ce “………….DA YIN HASSADA, TA KAI GA WUCE IYAKA” [Sahihul jami’I].

(7). NASIHA ZUWA GA MAI HASSADA:-
Ya kai mai hassada ka sani lallai ni’imar da ke hannun mutane daga Allah subhanahu wata’ala ta ke.
Allah (SWA) ya ce “BABU WATA NI’IMA DA TA KE ZUWA MUKU, SAI DAGA WAJEN ALLAH.”
Allah shi ne wanda ya bawa wannan ya hana wancan, kuma ya fifita wancan akan wannan da arziki.
Allah ya ce “ALLAH SHI YA FIFITA SASHEN KU AKAN N ARZIKI”.

*YA KAI MAI HASSADA! Ya yin da ka ke Hassada wa mutum akan wata dukiya, matsayi ko ilimi! Ka sani wannan ni’imar daga Allah ne, yana bada ita ga wanda ya ga dama daga bayinsa, sai ya kasance kai mai hassada kana yaki da hukuncin Allah da kaddarawar sa. To ka ji Tsoron Allah. *YA KAI MAI HASSADA!! Ka ji tsoron Allah a karan kan ka, ka kuma yi tinani kadan, kuma ka duba idan wanda ka ke yi wa hassadar yana daga cikin ‘yan Aljannah, mai yasa za ka masa hassada akan wata ni’ima da duniya mai gushewa! Kuma zai tafi
zuwa ga Aljannah, fadin ta kamar fadin sammai da kassai.?!

*YA KAI MAI HASSADA!!! Ka ji tsoron Allah, ka yi tinani kadan, idan ya kasance wanda ka ke wa hassadar yana daga cikin ‘yan wuta, mai yasa za ka masa hassada akan wannan ni’imar ta duniya mai gushewa, kuma zai tafi zuwa wuta mai zafi (Allah ya tsare mu daga gare ta)?!

*YA KAI MAI HASSADA!!!! Shin za ka yarda wa kan ka abinda ka ke aikatawa mutane?! Ya kai mai hassada, ya makiyin ni’ima, shin za ka yarda wani ya yi ma ‘ya’yan ka hassada? Shin za ka yarda ayi wa dukiyar ka hassada? Shin za ka yarda wani ya yi wa aikin ka da ka ke yi hassada? Ko za ka yarda ayi maka? Ina tsammanin amsar da za ka bayar ta gaskiya ita ce A’A. Ba ka ji fadin Manzon Allah (SAW) ba! “IMANIN ‘DAYAN KU BA ZAI CIKA BA, HAR SAI YA SO WA ‘DAN UWAN SA ABINDA YAKE SO WA KANSA” [Riwayar Bukhari da Muslim].

(8). NASIHA GA WANDA AKA YI MA HASSADA:- ‘Yan uwa wajen soyayya don Allah! Abin fadi ga wanda aka masa hassada da mu gaba daya, da mai yin hassadar kan sa, Allah ya tsare mu da ku gaba daya.

Nasiha ga wanda aka yi masa hassada, wanda shine ma’abocin ni’ima ta dukiya ko ilimi ka wanin haka ita ce:-
*YA KAI WANDA A KA YI MA HASSADA: Idan kana son ka kasance a cikin kariya, ka yi tawakkali ga Allah shi kadai, ina jan hankalin ka ka da ka dogara ga wanin Allah. Allah (SWA) yana cewa: “DUK WANDA YA MIKA AL’AMARIN SA GA ALLAH, ZAI ISAR MASA” Abin nufi zai taimake shi ya kiyaye shi daga dukkan komai. Allah (SWA) ya sake cewa: “SHIN BA ALLAH BA NE MAI ISAR WA BAWAN SA” [Suratul Zumar].

*YA KAI WANDA AKA YI MA HASSADA: Kana son samun kariya? Ka nemi tsarin Allah daga masu Hassada, kamar yadda Allah ya umurce ka da cewa: “KUMA (ka tsare mu) DAGA SHARRIN MAI HASSADA YA YIN DA YAKE HASSADA” [Suratul Falaq Aya ta 5]. Manzon Ali ‘dalah (SAW) ya ce da Abdullahi ‘dan Abbas (RA): KA KIYAYE ALLAH, SAI YA KIYAYE KA, KA KIYAYE ALLAH SAI KA SAME SHI A GABANKA, KUMA IDAN ZA KA YI ROKO KA ROKI ALLAH, KUMA IDAN ZA KA NEMI TSARI KA NEMI TSARI DAGA ALLAH, KUMA KA SANI, LALLAI DA AL’UMMA ZA SU HADU AKAN SU AMFANAR DA KAI DA WANI ABU, BA ZA SU TABA AMFANAR DA KAI DA KOMAI BA, SAI DA ABIN DA ALLAH YA WAJABTA AKAN (zai same ka), KUMA DA ZA SU HADU SU CUTAR DA KAI DA WANI ABU, BA ZA SU CUTAR DA KAI DA KOMAI BA, SAI DA ABIN DA ALLAH YA WAJABTA AKAN KA (zai same ka), AN
DAUKE ALKALUMA, TAKARDU KUMA SUN BUSHE’. [Imam Tirmizi ya fidda shi].

*YA KAI WANDA AKA YI MA HASSADA: Kana son samun tsira daga daga masu hassada? Ina maka horo da yin zikirorin safiya da maraice, ka kuma yawanta ambaton Allah, sai ka zama ko da yaushe cikin kariya daga masu hassada.

*YA KAI WANDA AKA YI MA HASSADA:

Ka kare kan ka daga idon masu hassada, ta hanyar aqidah ingantacciya, domin aqida sahihiya za ta kare ka daga shaidanun Aljanu da mutane, za ta kuma kare ka daga mahassada.

HASSADA WADDA TA DA CE AYI:

Shine ka yi burin kai ma Allah ya ba ka irin misalin abin da ya bawa dan uwanka. Manzon Allah (SAW) ya ce: “BA HASSADA (wato hassada bata halatta) SAI CIKIN ABUBUWA BIYU: MUTUM NE ALLAH YA BASHI DUKIYA YANA CIYAR DA DUKIYAR TA HANYA MAI KYAU, DA KUMA MUTUMIN A ALLAH BA SHI, ILIMI YANA HUKUNCI DA ITA, KUMA YANA KARANTAR DA ITA” [Bukhari da Muslim].

KAMMALAWA.

Ina mai kira gare ku da ku yi gaggawa wajen aikata ayyuka na kwarai, domin gaggawa wajen aikata ayyuka na kwarai adon muminai ne, idan ka ga mutum yana da dukiya ka roka masa Allah ya kara masa dukiyar, kuma ya sanya albarka a dukiyar sa, kuma ka roki Allah kai ma ya ba ka irin nasa,idan ka ga mutum ya haddace Alqur’ani, sai ka roki Allah ya kara masa ilimi, kuma ka roki Allah ya sa kai ma ka zama irin sa, idan ka ga mutum yana da ‘ya’ya sun haddace ko suna kokarin haddace Alqur’ani, ka roki nemi taimakon Allah yasa ‘ya’yan ka su zama irin su.

Amma yin burin ni’imar ta gushe wannan dabi’ar shaidanne da yahudawa, da fasikai. Amma mumini wanda ya yarda da Allah sh ne abin bautawa, addinin Musulunci shine addini, kuma Annabi Muhammad Annabi ne kuma Manzon Allah, kuma wanda yake son aljannah, shi baya hassada wa mutane sai dai shi yana burin ya kasance irin su.

Ina godiya ga Allah a farko da karshe.

Wannan shine abin da ya sauwaka daga gare ni. Allah ya kare ni da ku daga yin hassada, ya kuma kare mu daga mahassada.

Alhamdulilahi rabbil Alamin.

Bawa fakiri mai neman gafarar Ubangijin sa tare da rahamar sa. MUHAMMAD MUHAMMAD ABUBAKAR.

(Albani Misau).

ko com.gmail@mukhair1434Email: ( ) mukhair2013@yahoo.com

Facebook: (Muhammad albani Misai)

Web site: albanimisau.blogsport.com

You might also like More from author

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...