Siyasa: Fulani Na Sauya Sheka Daga Jam’iyyar PDP Zuwa APC A Jihar Jigawa

8

Rahotanni daga kafafen yada labarai na Rediyo Jigawa na cewa daruruwan al-ummar Fulani da ke kauyen Kutugun a mazabar Sarawa wanda ke karkashin karamar hukumar Kafin Hausa sun sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

A jawabin da ya gabatar wajen karbar sabbin yan jamiyyar APC, Kwamishinan kudi Alhaji Umar Namadi yace gwamnatin APC daga sama har kasa ta kawo canji a fannonin tattalin arziki.

Yace gwamnatin jihar ta ware kudi naira biliyan N8 a kasafin kudin bana wajen kyautata rayuwar alummar jihar.

A jawabansu daban daban yan majalissar dokokin jiha Alhaji Muhammad Abdullahi Bulangu na mazabar Bulnagu da Alhaji Abdulwahab Toro Suleiman na mazabar Kafin Hausa sun taya su murnar shigowar jamiyyar APC.

Sun bayyana cewa, yankin yana amfana da ribar demokaradiyya ta gwamnatin jiha ciki hadda gudanar da aiyuka a jam’iyyar Sule Lamido ta Kafin Hausa da kuma aikin samar da ruwansha.

A nasa jawaban shugaban Miyetti Allah na yankin Ahmadu Babanbale da Abdullahi Ibrahim baban Iya sun bada tabbacin yin tafiya tare da kowa da kowa domin cigaban jam’iyyar

You might also like More from author

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...