Makarantar Ramadan: Manufofin Azumi A Musulunci

0 73
Ramadan
 Doktor Najib Auwal Abubakar, Jami’ar Bayero, Kano

Wannan rubutu zai yi tsokaci akan manufofin azumi a musulunci.

Ibadar azumi daya ce daga cikin ginshikan musulunci. An wajabta shi a shekara ta biyu bayan hijira, kuma Annabi (S.A.W) ya yi azumi na shekara tara kafin ya koma ga Allah.

Masana da dama sun tabbatar da cewa azumi tamkar wata makarantace da ta ke ilmantar tare da tarbiyyantar da wanda ya shigeta, don haka azumi ya kunshi canja ɗabiun me yinsa, tare da mayar dashi mutum na musamman.

 Ga kadan daga manufofin Azumi:

1. Tsoron Allah:

Wannan ita ce babbar munufar yin azumi kamar yadda Allah Ya fada a Suratul Baqarah aya ta 183: “Ya ku wadanda suka yi imani, an wajabta muku  yin azumi kamar yadda aka wajabta shi ga magabatanku, tabbas za ku samu tsoron Allah”.

A dunkule tsoron Allah shine mutum ya kiyaye dokokin Allah kamar yadda Allah ya ke so. To, so ake ka zama me tsoron Allah a rayuwarka baki ɗaya ba kawai cikin Ramadan ba.

2. Ikhlasi:

Azumi ya kunshi yin abu tsakani da Allah (Ikhlasi)  ba don mutane su gani su yaba ba.  Domin me azumi ko shi kadai ne a wuri ba ya taba karya azuminsa, saboda ya gamsu har zuciyarsa ya yi saboda Allah, kuma idan be gaya maka yana yin azumi ba to ba za ka taba ganewaba,  shi yasa Allah yace :Me Azumi yana barin Sha’awarsa da abincinsa domin Yardata, Azumi nawa ne, ni na san me zan bawa wanda ya yi (Bukhari). Don haka ka zama me yi don Allah.

3. Kulawa da tsari, da amfani da lokaci yadda ya kamata:

Hakika Allah Ya Sa lokaci na musamman don yin azumi, kuma baya halatta wani ya sabawa wannan lokaci (fitowar alfijir zuwa faduwar rana), kuma Annabi ya koyar da mu gaggauta buda baki, da jinkirta sahur. Duk wannan yana nuna tsari da kula da lokaci.

‘Yan uwa mu daure mu amfana da wannan makaranta ta azumi, ko ma rabauta a duniya da lahira.

Wassalam.

Malam Najib Auwal Abubakar

Jami’ar Bayero, Kano Najeriya

 

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...