Tarihi: Watan Ramadan Ya Kasance Wata Mai Tarihi

21

Watan Ramadan Watane mai Tarihi a cikin Musulunci wanda a cikinsa aka Samu da yawa daga cikin Nasarorin yaki da Kafirai. Gasu kamar haka:

Shekara Ta Farko: A cikin Ramadan aka aika Sariyya ta farko karkashin jagorancin Hamza bn Abdulmutallib, sai Sariyyan Ubaidah binil Harith, domin sanya tsoro a cikin zukatan Kafirai.

Shekara Ta 2: A cikin 17 ga watan Ramadan akayi Yakin Badar Alkubra.

Shekara Ta 3: A cikin Ramadan Manzon Allah Sallahu Alaihi Wasallam ya Shirya Runduna a garin Madinah domin su hana mushrikai da suke son daukan Fansan Yakin Badr.

Shekara Ta 5: Shiryawa Yakin Khandaq, anyi yakin ne a cikin watan Shawwal wato watan Sallah kamar yanda Imamu bn Qayyim ya ce sun shirya mashi da wata 1 wato suna hakka ganuwa.

Shekara Ta 6: Sariyyan Gaalib bin Abdullah wanda ta kunshi mutum 130 wanda sukayi nasara akan bani Abdullahi bn tha’alabah.

Shekara Ta 8: Bude Makkah a cikin 20 ga watan Ramadan. Allah ya daukaka Addininsa da Manzansa da muminai kuma ya tseratar da Dakinsa me alfarma daga Hannun Mushrikan Kuraishawa, Manzan Allah Sallalalhu Alaihi Wasallalm ya Shigeta tare dashi akwai Sojojin Musulunci 10,000.

Shekara Ta 13: Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam shi da Sahabbansa suka dawo daga Yakin Tabuka.

Shekara Ta 9: Yakin Buwaib ya kasance cikin watan Ramadan a wuri da ake kira Buwaib kusa da kufa, a yau a cikin kasar Iraq inda Farisawa karkashin jagorancin Mahran da musulmai Karkashin Jagorancin Almuthanna bin Harithah wanda yaki me matikar muni ya afku daga karshe Allah yaba musulmai nasara, an kashe da dama daga cikin musulmi, sukuma Farisawa tsakanin wanda aka kashe da wanda suka fada cikin ruwan Furat wajen gudu kimanin 100,000 kuma aka samu Ganima me yawa, daganan ne aka karya Lagwan Farisawa. Sannan sai Bude Garin Nuuba, a kudancin masarkarkashin Jagorancin Abdullahi bin Sa’ad bin Abi Sarah, wanda hakan ya bude kofa ga muslunci wajen Yad’uwa a garuruwa da yawa.

Shekar Ta 53: Bude TsibirinRuuds, a karkashin Junadah bn Abi Umaiyah.

Shekar Ta 67: Aka Gusar da daular Mukhtar Athak’afi wanda aka kashe a 14 ga ramadan karkashin jagorancin Gwamnan Basra Mus’ab bini Zubair.

Shekar Ta 91: Bude Andalus a hannun Darik’ bin Yazid bawan Musa dan Nusair sannan se Yakin Durif, musa bin Nusair ya aika wani mutum daga cikin K’abilar Bar-Bar ana kiransa Duraif da mutane 400 da dawakai 100, inda suka tafi suka kai farmaki a gefen tekun Andalus kuma suka dawo da nasara.

Shekara Ta 102: Musulmai suka bud’e Faransa bayan sun kafu a Andalus wato Spain kenan, se suka fara yakan Arewaci da yak’I abayan duwatsun pranis wanda suke tsakaninn Andalus da Faransa wanda da yawa daga cikin dakaru suka jagoranta. Acikin dan wannan gajeren lokaci baze yiwu mu iya ambatan duk yakin da’akayi cikin Ramadana ba ko bayanai sosai gameda hakan, kawai munso bayyana wasu daga cikine kawai dan nuna muhimmancin wannan wata da tarihinsa wajen musulmi.

You might also like More from author

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...