Dubai Za Ta Fara Amfani Da Motoci Masu Tuka Kansu Wajen Gano Masu Laifi

26

Rundunar ‘yan sandan Dubai da ke kasar UAE ta ce za ta fara amfani da wata karamar mota mai tuka kanta wajen sintiri akan titina domin nemo masu laifi.

Motar dai na dauke ne da fasahar iya gano fuskar kowanne mutum da ta yi ido biyu da shi.

Wannan batu na kunshe ne a wata sanarwa da rundunar ta fitar da ke bayyana kudirin ta na sauya tsarin yadda ta ke gudanar da ayyukanta.

Sai dai rundunar ta ce wannan fasaha fa ba a fitar da ita bane domin maye gurbin ayyukan mutum da na injina, illa kawai domin ta ragewa mutane aiki.

A wajen gwajin fasahar motar, an nuna cewa motar na dauke da kananan jiragen nan marasa matuki da ake kira ‘Drones’, wadanda za su na shiga surkukin da mota ko jami’an tsaro ba za su iya shiga ba.

Sai dai ba a bayyana ko wannan mota za ta na gano masu laifin ne kawai ko kuma za ta na kama su kamar yadda ‘yan sanda ke yi ba.

 

You might also like More from author

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...