Samfurin Wayoyin Da Za Su Daina Whatsapp Daga Karshen Shekarar Nan

1 46

Tun a watan Maris din shekarr 2016 ne kamfanin da ya mallaki manhajar WhatsApp ya sanar da dakatar da aiki da kirar wayoyin Blackberry

Daga bisani kamfanin ya tsawaita wa’adin zuwa watan Yunin 2017 kafin ya sake tsawaitawa zuwa karshen shekarar nan.

Samfurin wayoyin sun hada da Blackberry kirar Z10 da Curve da kuma Nokia S40 da suka kunshi Asha da X2 da C3 da kuma Lumia 520.

Sai kuma kirar Nokia S60 da sauran wayoyin da ke amfani da tsohon tsarin Android wanda kamfanin ya daina amfani da su tun a karshen watan da ya gabata.

A jiya Laraba, masu amfani da wayoyin Blackberry sun wayi gari Whatsapp din su ya daina, inda suka fara tunanin ko wa’adin ne ya cika.

Daga bisani aka gano cewa rashin sabunta (update) manhajar ne ya haifar da haka.

 

1 Comment

  1. shafiu umar says

    Your comment …ya allah katemake musulunci da musulmai. kuma ka karya kafurai da kafurci ya allah kabamu lafiya da zama lafiya

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...