Lagwada: Yadda Zaki Sarrafa Gashahen Kifi

0 127

Gashashen Kifi/ Grilled Fish

Kayan Hadi:
1. Kiyin Karfasa / Tilapia
2. Albasa, lemun Tsami, Citta, Kanunfari, Masoro, Tafarnuwa, Garin Yaji ko Tarugu. 
3. Maggin Knorr, Gishiri, Kori, Thyme, da kayan Qamshi da Dandano
4. Myan Gyada.

Yadda Zaki Sarrafa: Ki wanke kifin ki ciki da bai, saka hannu har cikin bakin kifin ki wanke shi sosai. Bayan kin wanke sai ki tsane ruwan in sauri kike yi kisa towel ko tissue ki cire ruwan.

Daga nan sai ki daka ko kiyi blending kanunfari da masoro, citta, thyme, da sauran su. In kuma kina da garin su shikenan. Sai ki juye a mixing bowl.

Sannan ki dauko albasa kamar rabi haka ki saka, ki zuba tafarnuwa biyu manya, idan ginger ne dake to a cikin nan ne zaki hada shi, sai ki yi blending ko daka yayi luqui luqui. Haka nan in tarugu ne dake ba garin yaji ba a nan zaki saka shi.

Daga nan sai ki juye duka hadin a wuri daya, ki zuba curry kadan, ki zuba knorr da gishiri, sannan ki matse lemun tsami qaramin cokali daya ki zuba. Sai ki zuba oil yanda hadin zai kama jikin kifin.

Bayan kin jujjuya sai ki yiwa kifin tsagu tsagu (gashes) a jikin sa kamar guda biyu zuwa uku, gaba da baya yanda ruwan hadin zai shiga ciki. Sai ki zuba masa dukkan hadin yaji sosai ya kama, ragowar ma duka ki zuba a kansa, sai ki saka a fridge yayi kamar minti 30 in a freezer ne so ake kayan hadin da ke jikinsa su bushe a jikin ba wai yayi qanqara ba.

Daga nan kuma sai kiyi gashi in baki da oven ki tada rushi ki sa abu mai raga raga sai ki daura kifin ki, kina yi kina jujjuya wa har ya gazu.

Hadin Sauce/Sauce

Kayan Hadi:
1. Albasa biyu ko uku
2. Tarugu, Tattasai da Green pepper
3. Tafarnuwa 1
4. Gishiri da Maggi knorr

Yadda Zaki Hada Sauce: Farko zaki yanka albasanki da tattasai da green pepper shape da kike so amma dan manya, sai ki daura mai a tukunya kamar quater qaramin ludayi, in yayi zafi ki zuba albasan da tattasan, ki yi ta juyawa, daga nan sai ki zuba niqaqqen tarugu biyu ko garin yaji da tafarnuwa tare da sinadarai, sai ki dan zuba ruwa kadan yanda zasu dahu. Zaki ga ya dahu shi bai dahu can ba, shi kuma ba danye ba wato daidai wa daida.

Daga nan kifin ki ya gasu in kina so sai kawai ki zuba wannan sauce din a sama. Ai haka zaki ji kawai yana shigewa cikin tumbin maigida yana santi.

Kada a manta a ajiye wa mai gida lemun tsami na wanke hannu bayan ya gama ci saboda qarni. Sannan a tabbata an saka ginger ko citta, tafarnuwa da kanunfari don suna da muhimmanci a gashi.

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...