Yadda Ake Girka Miyar Ruwan Kwakwa

0 172

Kayan Hadi

 1. Ruwan markadaddiyar kwakwa
 2. Naman cinyoyin kaza
 3. Kore da jan tattasai
 4. Albasa
 5. Karas
 6. Koren wake
 7. Corn starch
 8. Citta
 9. Kori da Thyme
 10. Kayan Dandano
 11. Man gyada
 12. Attaruhu

Yadda Ake Sarrafawa

1. Za a yayyanka cinyar kazar a cire kashin. A hada ruwan kori da thyme da attaruhu da kayan dandano a zuba kazar a ciki a ajiye zuwa anjima, wato a yi ‘marinating‘ din shi

2. A yayyanka Kayan lambu; Koren tattasai, karas, albasa, a nika danyen citta a ajiye a gefe

3. A samu ruwan da aka tace daga nikakkiyar kwakwa a hada da corn starch har sai ya yi kauri

4. A zuba mai a cikin tukunya, a soya albasa. Sai a zuba naman kazan da aka yi marinating a soya shi sama sama

5. Idan naman kazar ya yi ja, sai a zuba ruwan kwakwar da aka kwaba da corn starch a kai, a yi ta juyawa. Za a ga ya kirtibe ya yi kauri. Idan kaurin ya yi yawa za a iya kara ruwa.

6. A zuba kayan lambun da aka yayyanka; karas, tattasai, albasa, koren wake, da markadaddiyar citta

7. A bar shi har sai naman kazar da kayan lambun sun dahu

8. Ana ci da shinkafa ko Taliya

A ci dadi lafiya

 

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...