Gulma Da Duminta Daga Duniyar Kwallon Kafa

0 202

 

Barcelona ta ce a shirye ta ke da ta biya fam miliyan 120 don daukar dan wasan tsakiya na Liverpool, Philippe Coutinho, mai shekaru 25don zama madadi ga Neymar

 

 

Duk da furucin da kocin Liverpool, Jurgen Klopp ya yi na cewa ba zai sayar da Coutinho ga Barcelona ba duk tsiya, ita kuma Barcelona a nata bangaren na da yakinin kammala cinikin dan wasan a cikin makon nan

 

 

Barcelona za ta yi amfani da wani bangare na kudin da ta samu daga cinikin Neymar wajen sayen Julian Draxler mai shekaru 23 daga PSG. Tuni dai har an hango manajan Draxler din a Barcelona

 

Jurgen Kloop ya ce a shirye ya ke da ya dakata da neman Virgil van Dijk na Southampton sakamakon kwan gaba-kwan baya da ke cikin cinikin sayen dan wasan. Klopp ya bayyana cewa zai ci gaba da amfani da ‘yan wasansa masu buga masa baya ba tare da ya kawo wani canji ba

 

 

Kocin Arsenal, Arsene Wenger ya bayyana cewa ‘yan wasan tawagar sun yi masa yawa a yanzu, a saboda haka, za a sayar da wasu kafin a rufe kasuwar saye da sayarwan ‘yan wasa

 

 

Alexis Sanchez zai hakura ya karasa shekara dayan da ya rage masa na kwantiraginsa da Arsenal sakamakon kin sayar da shi da Arsenal ta yi. Sanchez din zai bar Arsenal a karshen kaka mai zuwa bayan ya kammala da Arsenal

 

 

 

Barcelona ta kammala shiga yarjejeniya da dan wasan tsakiya na Borussia Dortmund, Ousmane Dembele mai shekaru 20 wanda rahotanni suka bayyana cewa Dortmund za ta sallama shi ne akan fam miliyan 90.2

 

 

Haka kuma dai, Barcelona ta yi nisa wajen tattauna batun kawo tsohon dan wasan tsakiya na Tottenham kuma dan wasan kungiyar Guangzhou Evergrande a yanzu wato Paulinho mai shekaru 29

 

 

Chelsea za ta shiga gasa da Manchester United wajen daukar dan wasan gaba na Real Madrid, Gareth Bale mai shekaru 28 da aka ce darajarsa za ta kai fam miliyan 90

 

 

Chelsea, Manchester United da Monaco na da ra’ayin sayen dan wasan  baya na Barcelona, Sergi Roberto wanda Barcelonar za ta yi wa kudi na fam miliyan 36.1

 

 

Kocin Manchester United, Jose Mourinho na so hukumomi a kungiyar da su sayo masa dan wasan baya mai buga numba 2 na Monaco, Fabinho mai shekaru 23

 

 

Daraktan wasanni na kungiyar AC Milan ya musanta rade-radin da ake yi na cewa kungiyar za ta sayi Zlatan Ibrahimovic da zarar ya kammala jinyar da ya ke yi

 

 

Bayan rasa Nemanja Matic da kocin Chelsea ya yi ga Manchester United, wanda hakan ya faru ne ba a son ransa ba, Antonio Conte ya bayyana cewa ba shi da wani karfi na hana kungiyar sayar da Eden Hazard wanda Barcelona ke nema ruwa a jallo

 

 

Dan wasan tsakiya na Manchester City, David Silva ya fara tattauna batun komawarsa kungiyar Las Palmas, wacce ke a mahaifarsa ta Gran Canaria. Amma batun komawar tasa Las Palmas, zai faru ne bayan kwantiraginsa da Man City ya kare a shekarar 2019

 

 

A karo na uku, Leicester City ta ki amincewa da tayin da AS Roma ta mika mata na fam miliyan 35 don sayen Riyad Mahrez mai shekaru 26

 

 

Pierre-Emerick Aubameyang mai shekaru 28 ya bayyana cewa ya yi wata ganawa da hukumomi a kungiyarsa ta Borussia Dortmund akan batun barinsa kungiyar, sai dai kuma bayan tattaunawar ne sai ya canja ra’ayinsa na son barin kungiyar a bana

 

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...