Yadda Rayuwar Dan Adam Za Ta Kasance a Shekarar 2050

0 87

Wani sanannen farfesa a fannin kwakwalwar kwamfuta, farfesa Toby Walsh ya yi hasashe akan yadda kwamfutoci za su sauya fasalin rayuwar dan adam ta yau da kullum nan da shekarar 2015.

A wani littafinsa da ya kira “It’s Alive: Artificial intelligence from logic piano to killer robots”, farfesan ya ce za a samu sauye sauye a fannonin sifiri, kiwon lafiya da nishadi.

A cewar farfesan, nan da 2050 za a haramtawa mutane tukin mota, wanda hakan zai yi matukar rage hatsarurukan da ake samu saboda kasada irin ta dan Adam.

Motoci masu tuka kansu ne za su mamaye duniya.

Farfesan ya ce a kullum za a na ziyartar likita, kuma wannan likita ba wani abu bane illa kwamfuta mai kwakwalwa irin ta dan adam.

Ya ce mutane za su na saka na’urori masu kama da agogo a hannunsu da a koda yaushe ke lura da lafiyar su.

Shadda za ta iya duba lafiyar mutum ta hanyar tantance bahaya da fitsarin da aka yi a cikin ta.

Haka zalika wayoyin hannun za su na daukan hotunan mutane da nufin dubawa ko akwai wani abu da ke damun su.

A fannin nishadi, farfesan ya ce gyamagyamai za su maye gurbin fina finai, ta yadda mutum zai iya yin kallo amma shi zai kayyade yadda karshen zai kasance.

Walsh ya ce nan da wannan lokaci, za a bar kwamfutoci da aikin dauka da korar ma’aikata.

Mutane za su na yi wa dakunan su magana kuma su na samun amsa. Ya ce na’uarar da za ta na bada masar za ta iya kasancewa firji, talabijin, rimot da sauransu.

Mutum zai bukaci na’urar ta yi kananan abubuwa kamar su kunna kwan lantarki, ko ya tambaye ta abubuwan da ke kan shafukan yanar gizo.

Sai dai farfesan ya ce mutane da dama za su yi adawa da wadannan sauye sauye, yayin da wasu za su rungume su hannu biyu biyu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...