Mai Kungiyar Chelsea, Roman Abramovich Ya Sake Sakin Matarsa

0 96

Attajirin nan dan asalin kasar Rasha kuma mamallakin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Roman Abramovich ya raba gari da mai dakinsa, Dasha Zhukova, da suka shafe shekaru 10 tare

 

Abramovich, wanda shi ne mai arziki na 139 a duniya da kimar dukiyarsa ta kai dalar Amurka biliyan 9.1, na da ‘ya’ya biyu da Dasha

 

Ma’auratan biyu sun tabbatar da batun rabuwar tasu a wata sanarwa ta hadin gwiwa da suka fitar a jiya Litinin

 

abrahamovic and dasha.PNG

 

Wani bangare na sanarwar ya kasance kamar haka: “Bayan shafe shekaru 10 tare muna zaman auratayya, mun yanke wani hukunci mai matukar wahala na kawo karshen aurenmu, sai dai za mu ci gaba da kasancewa abokan juna na kusa, iyaye ga ‘ya’yanmu, kuma abokan hulda a kasuwancin da muka shiga na hadin gwiwa. Mun yi alkawarin kulawa da ‘ya’yanmu tare”

 

Wannan dai shi ne karo na uku da Abramovich ke sakin matarsa. Matarsa ta fari, Olga Yurevna Lysova, ya aure ta ne a shekarar 1987 kuma sun rabu a shekarar 1990 ba tare da sun samu haihuwa tare ba. Sai ya auri Irina Malandina a shekarar 1991, wacce ta haifa masa ‘ya’ya biyar kuma suka rabu a shekarar 2007 bayan labari da ya zo wa Irina mijinta na soyayya da Dasha wacce ita ma ya rabu da ita jiya

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...