Gulma Da Duminta Daga Duniyar Kwallon Kafa

Labarai Daga Duniyar Kwallon Kafa

0 534

 

Barcelona na sa ran kammala cinikin Philippe Coutinho a karshen makon nan duk kuwa da tirjiya da suke samu daga hukumomi a kungiyar Liverpool na kokarin hana Coutinho komawa Barca. Tuni dai Barcelona ta aike da wata tawaga Ingila don tabbatar da cinikin Coutinho ko da kuwa farashinsa zai kai fam miliyan 120

 

Shugaban Hukumar gudanarwar Real Madrid, Florentino Perez ya fadawa manema labarai da babbar murya cewa Gareth Bale ba na sayarwa bane sakamakon zawarcin dan wasan da Machester United ke yi

 

Sai dai kuma sashenmu na gulma da duminta ya gano cewa, Florentina Perez din ya fadawa kocin Manchester United, Jose Mourinho cewa a shirye ya ke da ya sayar da Bale din

 

Chelsea ta sake farfado da batun sayen Alex Oxlade-Chamberlain daga Arsenal, inda suka saka masa fam miliyan 25

Antonio Conte ya shiga neman dan wasan baya na Tottenham Danny Rose

 

Manchester City ta tuntubi Barcelona ko za ta sayar mata da Sergio Busquests mai shekaru 29

 

Inter Milan ta shiga zawarcin Riyad Mahrez bayan da Leicester ta ki sallamawa Roma shi a karo na uku akan fam miliyan 32. Leicester dai ta dage akan sai an sayi dan wasan akan fam miliyan 50

 

PSG ta shirya tsaf don ta biya fam miliyan 80 don daukar Alexis Sanchez a wani kokarin na doke Manchester City a gasar daukar dan wasan

 

PSG ta karfafawa Manchester United da Chelsea gwiwa bayan da ta bayyana cewa za ta sayar da Serge Aurier

 

Southampton ta shiryi barin Virgil van Dijk ya rube a benci akan su sayar da dan wasan

 

 

Akwau rade-radin cewa, Ahmad Musa na Nijeriya da Leicester City zai koma Hull City kafin a rufe kasuwar saye da sayarwan ‘yan wasa

 

Bayan rashin nasara da Manchester United ta yi akan Real Madrid a cin kofin Super Cup a daren jiya, Jose Mourinho ya ware Nemanja Matic a matsayin dan wasan da ya fi taka rawar gani a cikin ‘yan wasan da suka doka wasan

 

Manchester united za ta sake gwada mika wani tayin ga Inter Milan don daukar Ivan Perisic

 

Borussia Dortmund sun fadawa Barcelona cewa in har suna son daukar Ousmane Dembele to fa sai sun ajiye fam miliyan 135

 

Marouane Fellaini

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...