An Gargadi Maza Da Su Daina Shan Nonon Matansu Da Ke Shayarwa

Iyaye Maza Su Bar Wa Jariransu Nonon Uwa Akalla Na Watanni 6 Na Farkon Rayuwar Jariran

0 933

Kwamishinan yada labarai na jihar Legas, Steve Ayorinde ya gargadi iyaye maza, musamman masu dabi’ar nan na shan nonon matansu da ke shayarwa da su guji wannnan dabi’ar da ya kira da gasa da ‘ya’yan nasu

 

Kwamishinan ya bayyana hakan ne ta bakin tsohuwar shugabar kungiyar ‘yan jarida mata reshen jihar Legas, Madam Toro Oladapo a wajen taron wayar da kan mata masu shayarwa da kungiyar ‘yan jarida mata (NAWOJ) reshen jihar Legas ta shirya

 

Kwamishinan ya ci gaba da cewa a maimakon iyaye maza su ci gaba da gasar zukar nonon uwa da ‘ya’yanyensu da ake shayarwa, kamata ya yi su bar wa yaran, su kuma ci gaba da karfafa wa matayen nasu masu shayarwa gwiwar shayar da yaransu da ruwan nono haikan a tsakakkanin watanni shida na farkon rayuwar yaran

 

“Babu abinda zai inganta lafiya da girman jariri sama da nonon uwa. Madarar gwangwani da nonon dabbobi ba za su iya bayar da sinadaran da nonon uwa zai bayar ba”

 

“Na san za ku yarda da ni, in na ce, yaran da suka samu kulawar shayarwar nonon uwa da kyau, sun fi wadanda ba su samu ba hazaka da kwazo a harkar neman ilimi”

 

“A saboda haka na ke jan hankalin ‘yan jarida da su taimaka wajen yada muhimmancin shayar da nono ga jarirai don samun lafiyayyiyar al’umma”

 

Kwamishina ya kara da cewa, a baya dai iyaye mata na amfani da lokacin shayarwa wajen kayyade iyali da tazarar haihuwa ta yadda mace ba za ta dauki wani cikin ba har sai ta yaye dan da ta ke goyo

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...