Boko Haram Ta Yi Kurmus Da Garin Yumbuli A Madagali

0 163

Boko Haram ta kai wani mumunar hari yankin Madagali wanda suka kwashe awanni har uku suna kone garin Yumbuli a yayin da mutanen garin suka tsere.

Harin dai na jiya shine hari na hudu a mako guda da ‘yan Boko Haram suka kai garin Yumbuli a karamar hukumar Madagali a jihar Adamawa wanda ke kan iyaka da dajin Sambisa.

Alhaji Yusuf Muhammad, shugaban karamar hukumar Madagali ya bayyanawa manema labarai cewa abin da suka tarar abin takaici ne kuma abin kuka ne saboda duk garin gaba daya ‘yan Boko Haram suka kone. Sun kone gidajensu da abincinsu da dabbobinsu da duka kayansu. Babu wanda ya fita da komi illa abin da yake sanye dashi.

Alhaji Yusuf yace babu wanda aka kashe saboda duk sun gudu sun hau duwatsu, Madagali ce dai a jihar Adamawa ta fi shan wahala a hannun ‘yan Boko Haram, kullum sai an kashe mutane a yankin, mutanenmu basu iya zuwa gona, muna rokon gwamnati da ta taimaki mutanenmu kuma ta kara dakarun tsaro.

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...