Daliban Kwalejin Ilimi Sun Kashe Abokinsu Kan Zargin Luwadi A Jihar Jigawa

0 225

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan sandan jihar Jigawa sun cafke wasu dalibai guda 15 wanda ake zargi da kisan abokinsu a kwalejin ilimin Kimiyya da Fasaha ta gwamnati da ke karamar hukumar Kankarna a jihar Jigawa.

Jinjiri Audu, Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, ya tabbatarwa BBC faruwar wannan lamari yace daliban da aka kama ‘yan makarantar Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta gwamnati ce da ke karamar hukumar Karkarna, an kama su ne a ranar 8 ga watan nan.

Ya kara da cewa daliban na tsakanin shekara 17 zuwa 19, an yi zargin dukan da suka lakadawa abokin nasu ne ya yi ajalinsa. Sannan kuma suka dauki gawar mamacin, suka jefar ta a wani daji da ke kusa da makarantar a ranar 6 ga watan Agustar nan, da misalin karfe 2 da rabi na dare.

”Wadanda ake zargin sun kafa wani kwamitin ladabtar da mamacin, bayan sun yi zargin wai dan luwadi ne da safiyar wannan ranar suka yanke shawarar abin da za su yi suka dauke shi cikin daji, suka lakada masa duka da sanduna.”

“Bayan sun gama dukansa, sai suka dauko gawar tare da jefar da ita a dajin, sai da safe sannan hukumomin makarantar suka ga gawar”.

Jinjiri ya ce a asibiti ne likitoci suka tabbatar da mutuwarsa, jami’an tsaro na ci gaba da bincike kan lamarin kuma nan ba da jimawa ba, za a gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu.

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...