Wani Mutum Mai Shekaru 45 Ya Yi Wa Yaro Mai Shekaru 9 Fyaden Da Ya Zama Ajalinsa

0 249

Rundunar ‘yan sandan jahar Kebbi ta ce ta kama wani mutum mai suna Dantani dan shekara 45 a bisa zarginsa da ta ke yi da yi wa yaro mai shekaru 9 fyade wanda ya zama ajalinsa.

Lamarin ya faru ne a garin Zauro da ke jahar ta Kebbi.

Kwamishinan ‘yan sandan jahar, Ibrahim M. Kabiru, shi ya bayyana haka a taron manema labarai a jiya Alhamis.

Ya ce sun kama mutumin ne bayan da suka samu labarin cewa ya yi luwadi da wani yaro, Ibrahim Muhammad Dangi mai shekaru tara, lamarin da ya haddasa rasuwar shi.

Kwamishinan ya ce za su gurfanar da shi a gaban kotu a bisa tuhumar kisa.

A gefe guda, Kwamishinan ya ce sun kuma kama wasu maza biyu Ibrahim da Yohana a bisa zargin yi wa yara mata masu shekaru 10 da 12 fyade.

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...