Gwamnatin Saudiyya Ta Yankewa Wani Mutum Hukuncin Daurin Shekaru 13 Saboda Ya Yi Suka Ga Manufofinta

0 145

Kotu a kasar Saudiyya ta yankewa wani dan kasar hukuncin daurin shekaru 13 a gidan yari saboda yada manufofin Hezbolla a yayin da yake hudubar ranar Juma’a.

Kotun ta kama shi da laifin yin suka ga kasashen larabawa da kuma manufofin cikin gida na gwamnatin saudiyya.

Haka zalika kotun ta ce ta kama shi da laifin suka ga dokar kasar da ta hana a yi huduba akan wani abu da ka iya sa mutane su yi adawa da manufofin gwamnati.

Sai kuma laifin da ya aikata na wallafa hudubar ta shi a shafinsa na yanar gizo.

Banda hukuncin shekaru 13, kotun ta umarci a rufe shafin yanar gizon, sannan ta haramta masa fita daga kasar na tsahon shekaru 13 bayan ya kammala zaman yarin na shi.

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...