Hausawa Da Yarbawa Su Bar Mana Yankin Mu Kafin 1 Ga Watan Oktoba – ‘Yan Tada Kayan Baya Na Niger Delta

0 318

Gamayyar kungiyoyin ‘yan tada kayar baya a yankin Niger Delta sun bukaci hausawa da yarbawan yankin da su tattara inasu inasu su bar yankin nan da ranar daya ga watan Oktoba.

A wata sanarwa da gamayyar kungiyoyin suka fitar, sun kuma bukaci gwamnatin tarayya ta mayarda mallakin rijiyoyin mai mallakar yarbawa da hausawa ga ‘yan asalin yankin.

Haka kuma suna bukatar ma’aikatan kamfanonin mai da ke zaune a yankin da su ma su tattara ina su inasu su bar masu guri.

Kungiyoyin sun kuma ce su na bukatar gwamnati ta barsu su kafa ta su kasar mai suna Niger Delta Republic ko kuma a bar su su juya ma’adanan man fetur din su dari bisa dari ba tare da gwamnati ta sanya masu hannu ba.

Akan gaka ne suka ce daga ranar 10 ga watan satumba ba za su bar kowa ya kara diban man fetur daga yankin ba.

Kungiyoyin sunce za su dawo da fasa bututunan man fetur har sai gwamnati ta biya masu bukatunsu.

Kungiyoyin dai sun hada da Niger Delta Avengers, Niger Delta Volunteers, Niger Delta Peoples Fighters, Niger Delta warriors, Bakassi Freedom Fighters da Niger Delta Movement for Justice.

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...