Ko Wanene Miji Nagari?

0 314

Wanene Miji Nagari?

Miji na gari shi ne mutum mai ilimin addini kuma yake kwatanta aiki da iliminsa kuma ga shi da dabi’u masu kyau. Lallai babu shakka wanda duk Allah Yayi masa baiwar hada wadannan siffofi da dabi’u, Allah Yayi masa babbar kyauta, kuma wannan shi ne ake kira miji nagari.

Miji nagari shi ne wanda ya hada wasu siffofi guda goma (10) wadanda Allah Ta’ala ya ambata a cikin sura ta 33 aya ta 35 inda Allah Ya ambaci maza da mata nagari. Kuma shi ne wanda manzon Allah SAW da kansa yace idan ya nemi mace da nufin aure to lallai a bashi. Domin hana irin wadannan mazaje aure a lokacin da suka nema na iya sa iyayen yarinyar da ita kanta yarinyar su fada a cikin wata irin fitina da kuma barna a bayan kasa, haka dai fiyayyen halitta Annabin rahma SAW ya fada acikin ma’anar hadisinsa ingantacce.

Wasu Siffofin Maza Nagari Guda 10

  • Miji Nagari shine miji mai ilimi wanda ke kuma aiki da iliminsa
  • Miji Nagari shine miji mai kyawawan dabi’u
  • Ana gane miji nagari wajen alkhairinsa ga iyalansa domin wani hadisin manzon Allah SAW yace:”Mafi alkhairinku shine mafi alkhairi ga matansa”
  • Miji Nagari shine miji mai kyautatawa matarsa
  • Miji Nagari shine miji mai tausayin matarsa
  • Miji Nagari shine miji kishin matarsa
  • Miji Nagari shine miji mai girmama matarsa
  • Miji Nagari shine miji mai yaba kwalliyar matarsa
  • Miji Nagari shine miji mai yaba girkin matarsa
  • Miji Nagari shine miji mai yalwata kudin cefane domin a samu abinci mai dadiAllah Ya Bawa Mata Mazaje Nagari

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...