Kudaden Da Aka Gano A Wajen Diezani Dan Cikin Cokali Ne Akan Abinda Ta Wawushe -Magu

0 156

 

Shugaban Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) Ibrahim Magu ya ce makudan kudaden da hukumar ta gano daga hannun tsohuwar ministar man fetur Diezani Allison Madukwe bai kai cikin cokali ba daga cikin kudaden talakawan Nijeriya da ta yi rub da ciki akansu.

Magu yace bayan tsananta bincike kan zargin da ake yiwa ministar, hukumar EFCC ta gano tsabar kudaden da suka kai sama da naira biliyan 47 da kuma wasu Dala miliyan 487 da kuma tarin wasu gidaje da kadarori da ta mallaka.

Shugaban hukumar yace suna ci gaba da aiki da wasu hukumomin kasashen duniya domin gano wasu tarin dukiyar da tsohuwar ministar ta mallaka a can.

Tuni dai kasashen Amurka da Birtaniya su ma suka kaddamar da bincike kan ministar saboda zargin halarta kudaden haramun.

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...