Tattalin Arziki: Neja Za Ta Kafa Cibiyoyin Tabbatar Da Ingancin Kayayyakin Da Jihar Ke Fataucinsu Zuwa Kasashen Waje – Gwamna Sani Bello

0 127

Gwamnan jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello yayi kira da masu zuba hannu jari na kasar Amurka da sauran kasashen waje da su zo su zuba jari a jihar musamman a bangaroren daban daban da suka shafi harkar noma, albarkutun kasa, wasanni, da kuma yawan bude ido ko shakatawa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a taron harkokin kasuwanci na jihar Neja wanda aka gudunar a hukumar bunkasa harkar kasuwanci a yankunan Afirka da Carribbean wato African Carribbean Business Council of Greater Philadelphia(ACDBC) ta shirya garin Harrisburg da ke jihar Pennsylvania a kasar Amurka.

Gwamna Sani Bello ya ce gurinsa shine ya mayar da jihar Neja ta zama jihar da ake gudunar da harkokin kasuwanci na gida da waje musamman ma a bangaroren da suka shafi harkar noma, albarkutun kasa, kayayyakin aiki, yawon shakatawa da kuma wasanni inda yin hakan zai tabbatar da samar da gwamnati mai gaskiya da rikon amana

“Jihar Neja na tattare da dunbun damammaki da dama da kuma albarkatun kasa wadda masu zuba hannu jari za su amfana da su. Bayan haka kuma jihar na kusa da babban birnin tarayya Abuja, sannan Kuma muna da babu wata jiha a kasan Nijeriya da ta kai jihar ta mu fili – ingantacciyar kasar noma wanda ba a taba noma a kai ba. Ga mu da albarkatun kasa. Ga mu da yawan matasa sannan kuma da zama lafiya. Muna da Babban filin jirgin sama ta duniya. Jihar na hade da hanyar jirgin kasa da kuma tashar jiragen ruwa.

“Hakazalika, muna gina Gwamnati wacce zata jagoranci jama’a a cikin adalci, da gaskiya sannan kuma da muhalli mai maraba da masu zuba hannu jari.

” Gwamnan ya kafa kudirin a niyyar shine ya ga jihar Neja ta zama abun alfahari a duniya ta harkar fitar da man kade, inda ya bayyana cewa gwamnatin jihar na kokarin bude cibiyar da zata kula da kayayyakin da za a fitar zuwa kasashen waje wadda za ta hada kafada kafada da takwarorinta na duniya.

“Mun tatttauna da gwamnatin jihar Pennsylvania akan harkar kasuwanci da dama wandadan suka shafi bangaren noma, albarkatun kasa, wasanni da kuma yawon shakatawa. Muna bukatar taimako akan yadda zamu habbaka tattalin arzikin jihar. Yana da matukar mahimmanci ganin cewa jihar Pennsylvania itace jiha ta 6 wadda tafi kowace jeha tattalin arziki a kasar Amurka sannan kuma na itace na 18 a Duniya. Ina mai imani da cewa hadin gwiwa tsakanin jihar jihar Neja, da kasan Nijeriya, da kuma kungiyar kasashen rainon Pennsylvania zai taimaka sosai wajen habbaka tattalin jihohin.

“Muna bukatar wannan hadin gwiwan saboda mu inganta kimar kayyakin da mu ke fitarwa: a bangaren samarwa da sarrafawa, ajiya, tare da kasuwanci. Muna so mu kara yawan amfanin kasa da mu ke samarwa da kuma fasahar da za ta kara mana yawan amfanin kasa a filayen da muke girbewa; Muna bukatan injunan sarrafawa; da kuma ma’addanar kayayyaki; sannan kuma muna bukatar kasuwar da za ta siyar da za mi siyar da wadannan kayayyakin bayan mun gama sarrafa su.”.

A na shi jawabin, Gwamnan jihar Pennsylvania, Micheal Stack 111 ya bayyana cewa jihar sa a matsayin jihar wacce ta dogara da harkar noma, sannan kuma ya nuna sha’awar hada gwiwa da jihar Neja a harkar habbaka noma don riba. Ya kuma yi alkawarin zuba jari a harkar noman wanda zai kawo canji a jihar Neja ta bada kananan bashin bankuna.

A cikin tawagar da suka raka Gwamna Sani Bello halartar taron sun hada da dan majalisar jihar Neja mai wakiltar Bida 11, da shugaban kwamitin da ke kula da harkokin aiyuka, Hon. Mohammed Alhaji Haruna, da Shugaban ma’aikata na jihar Neja, Hon. Mikhail Al-Amin Bmitosahi, da Kwamishinan zuba jari, Hajiya Ramatu Yar’adua, da kwamishinan kudi, Hon. Ibrahim Balarabe, da kuma kwamishinan shari’a, Justice. Bar Nasara Danmallam.

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...