Wani Magidanci Ya Yasar Da ‘Ya’yansu 4 Sakamakon Talauci Da Ya Yi Masa Kanta

0 388

 

Wani magidanci ya yasar da ‘ya’yansa hudu a wani asibitin haihuwa, inda ya bar wata takarda tare da su na cewa ya yi iya duk mai yiwuwa, amma ba zai iya ci gaba da daukar dawainiyar ‘ya’yan nasa ba

 

Wannan lamari dai ya faru ne a karamar hukumar Agege ta jihar Legas kuma mutumin ya tafi ya bar ‘ya’yan nasa ne a wani asibitin karbar haihuwa ta karamar hukumar da ake kira da Area A Maternity Office

 

Tashar Agege TV ta rawaito cewa, a takardar da mutumin ya bari tare da ‘ya’yan nasa, ya bayyana cewa matarsa ta jima da guduwa ta bar shi sakamakon babu da ke damunsa

 

Sai dai kuma wani abin farin ciki shi ne, ko da aka mika yaran ga shugaban karamar hukumar Agege, Honarabul Ganiyu Kola Egunjobi, sai ya yi wa yaran tarba ta karamci tare da daukar alkawarin kulawa da yaran

 

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...