Wasu Daga Cikin Sojojin Da Ke Yakar Boko Haram Sun Koma Gida Wajen Iyalansu

0 220

Rundunar sojin Nijeriya ta aika wasu daga cikin jami’anta da ke yakar Boko Haram gida wajen iyalansu a garin fatakwal.

Jami’an daga sashe na 6 na bataliya ta 29 a rundunar ofireshon Lafiya Dole wadanda suka dade ne fiye da kima suna yakar ‘yan ta’addan.

Za a maye gurbinsu da sabbin jami’ai.

Wannan ya na kunshe ne a wata sanarwa da mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar, Aminu Iliyasu ya fitar a jiya Alhamis.

Ya ce an mayarda sojojin gida a bisa alkawarin shugaban rundunar sojin Nijeriya Tukur Buratai na mayarda wadanda suka jima a Ofireshon Lafiya Dole.

Lafiya Dole dai shi ne shirin rundunar na yaki da ta’addanci a yankin Arewa maso gabashin kasar nan.

Mista Iliyasu ya ce sojoji sun yi matukar bada gudunmawar su wajen kakkabe ‘yan ta’addan Boko Haram daga yankin.

An yi kira ga sojojin da su yi wa ‘yanuwansu da har yanzu suke cikin tsarin addu’ar kariya da samun nasara akan ‘yan ta’addan.

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...