Yaki Da Cin Hanci: EFCC Ta Kama Mutane 860 Wadanda Ake Tuhuma Da Zargin Almundahana

0 48

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta ce ta kama mutane fiye da 860 da ake tuhuma da hannu a almundahana cikin wata guda da bude ofishinta na Kaduna.

A cikin wata sanarwa, Shugaban Hukumar a shiyyar Kaduna Ibrahim Baffa, ya fitar ya ce an kama mutane 220, sakamakon korafe-korafe da aka shigar a gaban hukumar.

Baffa, ya ce kawo yanzu sun fara gudanar da bincike akan korafe-korafe 130 daga cikin 220, sun kuma shigar da karar 10 a gaban kotu.

Haka kuma ya ce sun samu nasarar kwato Naira miliyan 227 da kuma Dalar Amurka dubu 17 daga hannun wadanda ake tuhumar.

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...