An Biya Ta Diyyar Kimanin Naira Miliyan 31 Saboda ‘Yan Sanda Sun Fizge Hijabin Da Ke Kanta

0 205

Wata kotu a yankin Long Beach da ke New York a kasar Amurka ta bada umarnin a biya wannan mata dalar Amurka dubu 85,000, kimanin Naira miliyan 31 kenan a bisa cin zarafinta da ‘yan sanda suka yi na tube mata Hijabi da karfin tsiya.

Matar mai suna Kirsty Powell dai ta shiga hannun ‘yan sandan ne a lokacin da ta aikata wani dan karamin laifi da ba a bayyana ba a shekarar 2015.

‘Yan sandan duk maza sun fizge hijabin da ke kanta duk da cewa ta musu bayanin cewa ta saka ne saboda addininta ya bukaci haka.

Sannan suka tilasta mata daukan hoto ba tare da hijabin ba daga bisani suka sanyata ta kwana a cikin kurkuku a haka.

Bayanan karar da Powell ta shigar sun bayyana cewa ta shafe daren ta na kuka a sakamakon cin mutuncinta da na addininta da aka yi.

Kotun ta ce ta yarda da biyan diyyar ne saboda Powell ta na da hujja.

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...