Dalilin Da Ya Sa Muka Je Bincike Ofishin Majalisar Dinkin Duniya – Sojin Nijeriya

0 149

Rundunar sojin Nijeriya ta ce dakarunta sun gudanar da bincike a wani ofishin majalisar dinkin duniya ne saboda suna neman wasu manyan ‘yan Boko Haram.

Sai dai rundunar ta ce sam dakarun na ta ba su da masaniyar cewar ofishin mallakar MDD ne ba tunda babu wata alama da ta nuna hakan, illa dai kawai ya fada a cikin gidaje 30 da suka kai ziyarar bincike a lokacin.

Ta ce binciken ya biyo bayan wasu sahihan bayanai da ta samu da ke nuna cewa wasu manyan ‘yan Boko Haram sun yi satar shiga yankin Pompomari Bye Pass da ke jahar Borno.

A wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce binciken ya samu nasara duk da cewa ba ta kama kowa ba.

A jiya Juma’a ne dai MDD ta yi korafin cewa dakarun tsaro sun kai sumame kan daya daga cikin ofisoshinta a yankin arewa maso gabashin kasar, inda suka gudanar da bincike ba tare da izini ba.

Rahotanni sun bayyana cewa binciken da sojojin suka yi da sanyin safiyar jiya ya kai na tsahon awanni uku.

MDD dai na da yawan jami’ai a yankin Arewa maso gabashin kasar nan, inda ta ke bayar da tallafi ga mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa.

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...