Hukumar Sibil Difens Ta Tura Jami’anta 80 Zuwa Kudancin Kaduna

0 73

Hukumar tsaron farin kaya na reshen jihar Kaduan ta tura jami’anta kimanin 80 zuwa yankin kudancin Kaduna domin marawa tawagar dakarun tsaro ta Operation Safe Heave baya wajen aikin samar da tsaro a yankin.

Mai magana da yawun hukumar, Orndiir Terzungwe ya bayyana wannan a wata sanarwa da ya fitar a Kaduna.

Terzungwe, ya ce hadakar zata taimaka wajen hafaka tsaro da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Ya ce shugaban hukumar Alhaji Modu Bunu ya bukaci jami’an su zama masu kula da kuma kare hakin bil adama yayin da suke gudanar da aikinsu.

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...