Kotu Za Ta Yi Zama Akan Kiranyen Dino Melaye A Ranar 11 Ga Watan Satumba 2017

0 62

Babban Kotun Tarayya dake Abuja, ta sanar da ranar 11 ga watan Satumba a matsayin ranar da za ta yi zama kan batun kiranye da ‘yan mazabar Kogi ta yamma ke kokarin yiwa dan majalisarsu Dino Melaye.

Mai shari’a Nnamdi Dimgba, na kotun ya sanar da haka a bayan ya saurari lauyoyin bangarorin biyu inda suka tafka muhawara akan batun.

Wannan na zuwa ne bayan Melaye, ya shigar da kara inda ya kalubalanci sanya hannun wasu daga cikin mutanen da suka sanya hannun amincewa da kiranyen.

Al’ummomin yankin dai sun yanke hukuncin yiwa dan majalisar kiranye ne bayan sun yi zargin cewa bai musu wakilci na gari a majalisar dattawa.

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...