Lafiyar Buhari: Fadar Sugaban Kasa Ta Yaba Da Kalaman Majalisar Dattawa

0 110

Fadar shugaban kasa ta yabawa majalisar dattawa na kasa a bisa bayanin da ta yi na cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari bai sabawa doka ba a tafiyar sa neman lafiya da ya yi zuwa kasar Burtaniya.

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin majalisun dokoki, Ita Enang, ya sanar da haka a lokacin da yake magana da ‘yan jaridu a fadar shugaban kasa dake Babban Birnin Tarayya Abuja.

Ya ce majalisar ta fayyacewa wasu marasa kishin kasa masu fifita bukatun kansu bisa na kasa, cewa hakan da shugaba Buhari ya yi ba laifi bane.

Enang, ya ce kundin tsarin mulki y aba shugaban kasa damar tafiya neman magani ba tare da bashi lokacin dawowa ba, matukar ya sanar da majalisun dokoki.

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...