Mutane Fiye Da 41 Sun Rasu a Hatsarin Jirgin Kasa a Misra

0 61

Jiragen kasa guda biyu ne suka yi karo da juna a Arewacin kasar Misra a jiya, inda suka yi sanadiyar rasuwar akalla mutane 41 tare da jikkata fiye da 120.

Jiragen daya ya taso daga babban birnin kasar Cairo, daya kuma daga Port Said sun yi karone ne da misalin karfe 1:15 na rana a jiya.

Duk da cewa har hanzu babu tabbacin abun da ya haifar da hatsarin, rahotanni sun bayyana cewa daya daga cikin jiragen ne ya toshe hanya bayan da ya samu matsala.

Irin wannan mummunan hatsarin jirgin kasa dai ba kasafai yake faruwa a kasar Misra ba.

Shugaban kasar, Abdel Fattah al-Sisi ya bada umarnin a yi bincike game da musabbabin faruwar hatsarin, ya kuma yi alkawarin biyan wadanda abun ya shafa diyya.

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...