Barka Da Juma’a: Sakon Zance na GASKIYA daga Zauren Fiqhu

0 333

★Cikakkiyar nutsuwar ruhi ta tabbata ga mutumin da tunanin laifukansa ya hanashi hangen laifin wani.

 

★ Kaifin Hankali ya tabbata ga mutumin da yayi aiki da ilimin da ya sani, komai Qankantarsa, kuma ya sanya tsoron Allah adukkan lamuransa.

 

★ Murna da annashuwa sun tabbata ga Mutumin da Tunanin hisabi ya hanashi tara dukiya ta hanyar Haramun.

 

★ Wadatar zuciya ta tabbata ga mutumin da kullum yake gode ma Allah akan kowacce baiwar da yayi masa komai kankantarta, kuma ba ya kaiwa Qarar Ubangiji awajen halittunsa.

 

★ Cikar buri ya tabbata ga Mutumin da kwadayin gamuwarsa da Allah a Lahira ya hanashi dogon burin Zaman duniya.

 

★ ‘Dandanon zakin imani ya tabbata ga mutumin da ya fifita Son Allah da Manzonsa akan komai na duniya da lahira.

 

★ Lada mai yawa ya tabbata ga Mutumin da ya ji kalmar gaskiya (kamar irin wannan daga ZAUREN FIQHU) kuma ya isar da ita izuwa zukatan al’umma ba tare da jirkita komai a cikinsa ba.

 

Zauren Fiqhu

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...