WASAN SHARO NA FULANI

0 419

Sharo ko shadi wani wasane na fulani sukeyi a Arewancin Nigeria, su kanyi sharo da Tsumagiya ko kulki na kanya kokuma Geza. Sukanyi shadine lokacin kaka da bazara a duk shekara, sunayin shadinne domin nuna al, adunsu na gargajiya, duk da haka sukan nuna bajinta, jarumtaka da asiri.

 

 

Lokacin wasan sharo Fulani kan gaiyato yan uwansu Fulani daga sassa kasa kai hardaga kasashen dake makwaftka dasu kamarsu kamaru, Nijar da kuma chadi.Ta hanyar sharone sukan gane jarumin gaske a’tsakaninsu kaiharma awani lokaci saikayi wasan sharo da  zaka samu Auren Bafulatana, domin basasan bayarda yarsu ga Rago
Indan anzo filin daga duk Fulani da aka gaiyato sun hallarta tare da  ya”yansu, matansu, abokan karawa, makadansu da yan”kallo, yan wasan zasu tube kayansu domin yin damara daga susai gageran wando, zasu daura buzu ko zani agindinsu anai musu kida da waka kowa daga cikinsu anaimasa takyansa, sukuma suna ihu da kirari.

 

 

Abokin wasa zai doki abokin karawarsa da Tsumagiya ko kulki akiriji, Hakarkari ko ciki sau biyu zuwa sau goma acikin filin wasa yadanganta da yadda sukai alkawari. Duk wanda yanuna bajinta da Jarumtaka zaisami kudi, Mata ko kuma yayisuna, amma wadansu yan’’ wasan har mutuwa sukanyi.
“Matsoraci bashi zama gwani kowanene inji marigayi Alhaji Manman Shata Katsina Allah yagafarta masa amin”

 

Daga Sanusi Garba
garsanus2002@yahoo.com
08025892276

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...